A kalla fararen hula 79, ciki har da yara 43 ne suka mutu, kuma wasu 38 suka ji rauni a harin jirage marasa matuƙa da dakarun RSF suka kai Kordofan ta Kudu, in ji hukumomin Sudan.
A cikin wata sanarwa, gwamnatin Jihar Kordofan ta Kudu ta ce mata hudu suna cikin waɗanda suka mutu a harin na ranar Alhamis a birnin Kalogi a yammacin Sudan.
Ta ce jiragen suk harba rokoki huɗu kan makarantar yara kanana, da asibiti da yankunan da ke cunkushe da mutane, tare da kwatanta lamarin a matsayin 'mummunan laifi' da Ƙungiyar Sudan People's Liberation Movement-North (SPLM-N), wacce ke tare da RSF, ta aikata.
Da farko hukumomi sun bayar da rahoton mutuwar mutane 8, ciki har da yara 6 da wani malami, kafin adadin wadanda suka mutu ya ƙaru zuwa 79.
Sun yi kira ga al'ummar duniya da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan’adam su ɗauki mataki mai tsauri kan hare-haren, su ayyana RSF a matsayin 'kungiyar 'yanta'adda', kuma su ɗauki matakin ɗaura alhakin abubuwan da suka faru kan abokan ƙawancensu saboda abin da suka bayyana a matsayin 'laifukan rashin imani'.
Allah wadai na MDD
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi Allah wadai da harin jirgin a matsayin 'mummunan keta haƙƙin yara'.
Ya ce fiye da yara 10 masu shekaru tsakanin biyar da bakwai suna cikin waɗanda suka mutu.
"Bai kamata yara kada su biyan farashin rikici ba. UNICEF na roƙon dukkan ɓangarorin su dakatar da waɗannan hare-hare nan take kuma su ba da damar isar da gajin jinƙai ga masu matuƙar buƙata ba tare da tsangwama ba," in ji wakilin UNICEF a Sudan, Sheldon Yett.
"Kashewa da raunana yara, da hare-hare kan makarantun yara da asibitoci, manyan keta haƙƙin yara ne."
UNICEF ya ce harin ya auku a 'lokacin da ake fama da tsananin tabarbarewar tsaro a faɗin jihohin Kordofan tun farkon watan Nuwamba, wanda ya janyo gudun hijira mai yawa da tsananta buƙatun agajin jinƙai'.
Ya lura cewa fiye da mutane 41,000 sun tsere wa tashin hankali a Kordofan ta Arewa da ta Kudu a cikin wata ɗaya da ya gabata.
Babu wani martani nan-take daga ƙungiyar 'yan tawayen game da harin.
Jihohin Kordofan guda uku — Arewa, Yamma da Kudu — sun shafe makonni suna fama da mummunan yaƙi tsakanin sojojin Sudan da RSF, wanda ya tilasta wa dubban mutane tserewa.
RSF na iko da duk jihohi biyar na yankin Darfur sai wasu sassa na Arewacin Darfur, yayin da sojojin kasar ke riƙe da mafi yawan sassan sauran jihohi 13, ciki har da babban birnin ƙasar Khartoum.
Yaƙi tsakanin sojojin Sudan da RSF, wadda ya ɓarke a Afrilu 2023, ya yi ajalin aƙalla mutane 40,000 kuma ya tilasta wa mutane miliyan 12 barin wuraren zamansu, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

















