‘Yan bindiga ɗauke da makamai sun kashe wasu Turkawa biyu da direban motarsu ɗan ƙasar Habasha a yayin da suke tafiyar yawon buɗe ido a Habasha, kamar yanda Jakadan Turkiyya a Addis Ababa ya bayyana.
Jakadan Berk Baran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa harin bindigar ya faru ne a safiyar ranar 12 ga Janairu a wani ƙauye da ke kusa da garin Tum a yankin kudu maso yammacin Habasha.
An gano lamarin ya rutsa da wasu mutum biyu ‘yan Turkiyya masu suna Erdogan Akbulak da Cengizhan Gungor, tare da direban su dan asalin ƙasar Habasha, a cewar Baran.
A cewar jakadan, mutane hudu ne 'yan kasar Turkiyya suke tafiya a cikin motoci biyu a lokacin harin.
Mutane biyu da ke cikin motar da ke gaba sun samu damar tserewa ba tare da sun ji rauni ba, bayan nan suka sanar da ofishin jakadancin ƙasarsu kan lamarin.
Baran ya ce an kai mutane biyun da suka tsira da kuma gawarwakin wadanda aka kashe zuwa Addis Ababa a safiyar Talata.
"Ana ci gaba da gudanar da bincike. Sannan ana ci gaba da kula da 'yan ƙasarmu a ofishin jakadancin, kuma za a aika da gawarwakin zuwa Istanbul a jirgin Turkish Airlines a daren yau, inda za su isa gobe da safe," in ji shi.
Haɗin kai da goyon baya
Jakadan ya ce hukumomin Habasha sun yi gaggawar kai dauki bayan harin.
"Bayan samun labarin, ma'aikatar harkokin wajen Habasha ta tuntube mu don isar da ta'aziyya da kuma fatan samun sauki cikin sauri ga waɗanda lamarin ya shafa.
An kafa wata rundunar aiki wadda ta kunshi ma'aikatun harkokin waje, da na yawon bude ido da na tsaro, da kuma sassan 'yan sanda na tarayya da na kananan hukumomi, don gudanar da bincike kan lamarin da kuma shirya jigilar 'yan ƙasarmu da gawarwakin zuwa Addis Ababa.
Hukumomin Habasha sun ba da haɗin kai da goyon baya mai ƙyau," in ji Baran.
Ya kara da cewa ana jiran sakamakon bincike kan waɗanda suka kai harin.
Baran ya kuma bayyana cewa, ana yawan kai hare-hare a yankin wanda masu yawon buɗe ido ke bi a duk shekara, ciki har da masu ziyara 'yan Turkiyya.
Ya shawarci matafiya da su gudunar da bincike kan yankunan da suke shirin ziyarta a gaba, kana ya kara da cewa, a shirye ofishin jakadancin Turkiyya yake wajen samar da bayanai da taimako ga 'yan ƙasar da suka tuntube shi kafin zuwa ko ina a Habasha.
Ƙazalika Baran ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka mutu kana ya yi fatan samun sauki ga waɗanda suka tsira.












