Ƙungiyar ECOWAS ta bayyana matuƙar damuwa bayan samun rahotannin yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ƙungiyar ta soki abin da ta kira “yunkurin da ya saɓa wa tsarin mulki” wanda ke nufin take wa jama’ar Benin muradunsu.
A cewar ECOWAS, duk wani yunƙurin karɓe mulki ta hanyar ƙarfi barazana ce kai tsaye ga mulkin dimokuraɗiyya da zaman lafiya a yankin.
Ecowas ɗin ta bukaci a mutunta tsarin mulkin Benin gaba ɗaya, tana mai jaddada cewa dole a kare tsare-tsaren dimokuraɗiyya a kowane hali.
ECOWAS ta kuma yaba wa Gwamnatin Benin da Rundunar Sojin Benin bisa gaggawar da suka yi wajen shawo kan lamarin da dawo da doka da oda.
Ta gargadi shugabannin da suka shirya wannan juyin mulkin kan cewa alhakin duk wata asarara rai ko dukiya zai rataya ne a wuyansu.
Yayin da ta sake nanata kudurinta na kare tsarin mulki a yankin, ECOWAS ta ce za ta ci gaba da mara wa Benin baya ta dukkan hanyoyin da suka dace ciki har da yiwuwar tura sojojinta na ko-ta-kwana na yanki don kare ikon kasar da tsarin mulkin ta.
ECOWAS ɗin ta kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankula tare da haɗa kai wajen ganin an tabbatar da kwanciyar hankali gaba ɗaya a Benin.















