Burkina Faso ta saki mambobi takwas na ƙungiyar International NGO Safety Organisation (INSO) bayan hukumomin ƙasar sun kama su tare da tsare su kan zarginsu da leƙen asiri, kamar yadda INSO ta sanar a ranar Jumma’a.
Gwamnatin Burkina Faso ta soke izinin kungiyoyi 21 da ke aiki a ƙasar a watan Yuli, ciki har da INSO mai hedkwata a ƙasar Holland.
A cikin sanarwar, INSO ta ce: 'Muna maraba da sakin abokan aikimmu cikin aminci, kuma muna gode wa goyon bayan da ya sa wannan ya yiwu.'
An kama mutanen tun a watan Yuli amma gwamnatin ta sanar da hakan ta bayyana hakan ne kawai a farkon Oktoba.
INSO ta fayyace a ranar Jumma'a cewa an sako ma'aikatanta a ƙarshen Oktoba.
Mutanen takwas sun haɗa da ɗan Faransa, wata yar Faransa da Senegal, wani ɗan Czech, ɗan Mali da kuma 'yan ƙasar Burkina Faso huɗu.
Ikirarin leƙen asiri
Hukumomin Burkina Faso sun bayyana cewa INSO ta tattara sannan ta mika bayanan tsaro masu muhimmanci game da ƙasar ga ƙasashen waje, kuma ta ce 'yan kungiyarsu sun ci gaba da aiki a boye duk da an haramta mata aikin.
INSO, wadda ba ta bayar da ƙarin bayani game da lamarin ba, na yin sharhi dangane da tsaro ga sauran kungiyoyin jinƙai.
'A matsayinta na ƙungiyar jinƙai, za mu ci gaba da sadaukarwa wajen tallafa wa ƙungiyoyin da ke rarraba agaji don isar da taimako cikin aminci ga duk masu bukata,' in ji ta.
A ƙarshen 2024, ƙawar Burkina Faso kuma maƙwabciyarta, Nijar, ma ta soke izinin INSO na aiki a ƙasarta.
















