| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Filin Jirgin Sama na Istanbul ya zama na biyu mafi hada-hada a Turai a 2025: Erdogan
Turkiyya ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da hanyoyin jiragen sama mafi girma a duniya, in ji Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
Filin Jirgin Sama na Istanbul ya zama na biyu mafi hada-hada a Turai a 2025: Erdogan
Hoton terminal na tashin jirage na kasa da kasa a Filin jirgin sama na Istanbul, ranar 14 ga Yuni, 2024. / Anadolu Agency
12 awanni baya

Filin Jirgin Sama na Istanbul shi ne na biyu mafi hada-hada a Turai a bara, kuma na bakwai a duniya, in ji Shugaba Recep Tayyip Erdogan a ranar Litinin.

Ya ce mutane sama da miliyan 84.5 ne suka bi ta filin jirgin a shekarar 2025, kamar yadda Erdogan ya faɗa a lokacin wani biki a Filin Jirgin Sama na Esenboga, a babban birnin ƙasar Ankara.

Ya bayyana cewa burin shiga kowace kusurwa na duniya, ya sanya Turkiyya zama ɗaya daga cikin kasashen da ke da hanyoyin jiragen sama mafi girma a duniya.

Ya jaddada cewa ta hanyar ƙara yawan kasashe daga 81 zuwa 175, Turkiyya ta zama ƙasa mafi yawan yarjeniyoyin jigilar jiragen sama a duniya.

A shekarar 2002, adadin fasinjojin da suka yi tafiya a jiragen cikin gida da na ƙasa da ƙasa a Turkiyya ya kai miliyan 34.5 kawai, amma a 2025 wannan adadi ya kai sama da miliyan 247, in ji shi.

Ƙaddamar da sabon titin sauka na uku da sabuwar hasumiya, zai sa adadin waɗanda za su iya mu’amala da Filin Jirgin Sama na Esenboga zai ƙaru daga miliyan 20 zuwa miliyan 30, in ji Erdogan.

Ya ce sabbin sassan filin jirgin, da ƙimarsu ta kai dala miliyan 347, an yi su ne ba tare da kashe kuɗi daga asusun gwamnati ba.