Hukumar Kula da Masu Ƙaura ta Duniya (IOM) ranar Laraba ta ce mutum fiye da 1,000 sun tsere daga gidajensu a Kudancin Kordofan cikin kwana biyu sakamakon ƙamari na rashin tsaro, a wani mataki na ta’azzarar rikici a yankin a makonnin baya bayan nan.
Ma’aikatan IOM sun ce mutum fiye da 590 sun tsere daga ƙauyen Karmojiya da ke kusa da Abbasiya tun daga ranar Talata. Kazalika mutum 235 sun tsere daga Qardard Amradami kusa da Talodi, yayin da aka kori mutum fiye da 160 daga Damik.
Haka kuma yaƙin na korar mutane daga babban birnin yankin. A ranar Talata kaɗai, mutum 185 sun tsere daga Kadugli zuwa yankin Abu Zabad da Yammacin Kordofan da kuma garin Sheikan a Arewacin Kordofan, a cewar IOM.
Rikicin ya yi ƙamari ne kwanaki kaɗan bayan hukumar ta IOC ta bayar da rahoto game da tserewar mutum 600 daga Kadugli Litinin yayin da mayaƙan Rapid Support Forces (RSF) suka ƙara ƙaimi wurin kai hare-hare a yankin.
Jihohi uku na yankin Kordofan —Arewa, Yamma da Kudu— sun daɗe suna fama da rashin tsaro sakamakon arangama tsakanin sojojin Sudan da mayaƙan RSF, lamarin da ya tilasta wa dubban mutane ficewa daga matsugunansu tare da ta’azzara halin rashin jinƙai a yankin.
Yanzu dai mayaƙan RSF nne suke riƙe da ikon dukkan jihohin da ke yankin Darfur, yayin da su kuma sojojin ƙasar suke da iko da sauran jihohi 13, cikinsu har da Khartoum, babban birnin Sudan.
Yaƙin Sudan, wanda ya ɓarke a watan Afrilun 2023, ya kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu, kana ba shi da alamar zuwa ƙarshe duk da tsoma bakin ƙasashen duniya.


















