| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Shugaba Mahama ya yaba wa Amurka kan cire harajin da ta sa kan kayayyakin gona na Ghana
Shugaban Ghana ya ce kayayyakin gona na Ghana waɗanda ake kaiwa Amurka da suka haɗa da koko, avokado, lemu, barkono, albasa da doya, a yanzu ba za a rinƙa saka musu haraji ba.
Shugaba Mahama ya yaba wa Amurka kan cire harajin da ta sa kan kayayyakin gona na Ghana
Shugaba Mahama ya yi wannan jinjina ne a jawabinsa a bikin Ranar Manoma ta 41 da aka gudanar a Ho da ke Jihar Volta. / John Mahama Facebook
6 Disamba 2025

Shugaba John Dramani Mahama ya yaba wa Gwamnatin Amurka saboda cire harajin da ta kakaba kan kayayyakin amfanin gona da ake shigowa da su daga Ghana.

Ya ce harajin da aka kakaba ya shafi kayayyakin noma kamar koko, avokado, lemu, barkono, albasa da doya, yana bayyana cewa janye wannan mataki na nufin kayayyakin Ghana da ake kaiwa kasuwar Amurka yanzu ba za su sake fuskantar wani haraji ba.

Shugaba Mahama ya yi wannan jinjina ne a jawabinsa a bikin Ranar Manoma ta 41 da aka gudanar a Ho da ke Jihar Volta.

“Ba mu biyan wani haraji. Yawan cinikayyar mu da Amurka a kayayyakin noma yanzu ya kai kusan dala miliyan 100, amma za mu iya ƙara wannan sosai saboda damar da suke ba mu,” in ji shi.

Ya shawarci masu aikin noma da su duba jerin kayayyakin noman Ghana da ake fitarwa zuwa Amurka, domin su ƙara inganta ƙarfin samar da su don fitarwa da kuma samun ƙarin kuɗaɗe.

Shugaba Mahama ya bayyana cewa noma yana da riba kuma yana ƙara samun kuɗi, shi ya sa har a matsayinsa na Shugaba, yana ci gaba da kasancewa a matsayin manomi.

Ya ƙarfafa dukkan masu mukami da jami’an gwamnati da su sayi fili su shuka miskin mai (oil palm).

Haka kuma shugaban ya ƙarfafa gwiwar masu riƙe da muƙaman gwamnati da su samu gona su shuka kwakwar manja.

“Idan ka yi kadada 10 ko 20 na kwakwar manja, za ka yi mamakin yadda zai ba ka kuɗi fiye da albashin da kake karɓa a duk shekara,” in ji shi.

Shugaban ya roki ’yan Ghana da su zuba jari a cikin noma kuma su yi ƙoƙarin samar da isasshen amfanin gona domin su ƙara samun kuɗin shiga.”

Rumbun Labarai
‘Yanta’adda sun kashe mutane 14 a arewa maso yammacin Kamaru, in ji gwamnati
Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF a Kudancin Kordofan
Uganda ta ba da umarnin katse intanet a yayin da ake gudanar da zaɓen shugaban ƙasa
Trachoma: Ta'azzarar amosanin ido da ke makanta mutane na ƙarfafa fafutukar dawo da gani a Afirka
Wasu wayoyin hannu da aka yi odarsu a shekarar 2010 sun isa Libya bayan shekaru 16
Mitumba: Sake tunani game da kasuwancin tufafin gwanjo a Afirka
Ɗaruruwan mutane sun tsere daga gidajensu a Kudancin Kordofan na Sudan sakamakon sabbin hare-hare
Gwamnatin Sudan ta koma Khartoum bayan fiye da shekaru biyu ana yaƙi
Nijar ta soke ayyukan ɗaruruwan ƙungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na ƙasashen waje
Guinea-Bissau ta haramta taron manema labarai 'ba tare da izini ba' domin guje wa tashin hankali
Yaƙin Sudan: Sojojin Sudan sun ce sun yi wa sojojin RSF asara a Darfur da Kordofan
Burkina Faso, Mali da Nijar sun yi tir da ɗauke Maduro da Amurka ta yi
Somalia ta musanta satar abincin agaji bayan Trump ya sanar da dakatar da taimako
Yaƙi a Sahel: Ƙalubalen da ke tattare da yaƙar ƙungiyoyin ta'addanci
An kama tsohon Ministan Kudi na Ghana Ken Ofori-Atta a Amurka
An daƙile yunƙurin kifar da gwamnatin Traore na Burkina Faso Traore: minista
Shugaban ƙasar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka Touadera ya samu nasarar yin wa’adi na uku
Kotun Kolin Guinea ta tabbatar da Doumbouya a matsayin wanda ya lashe zaben kasar
Benin da Nijar sun kori jakadun juna a matakin ramuwar gayya
Sabon rikici ya ɓarke tsakanin sojojin DRC da 'yantawayen M23 a kusa da wani babban gari