| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Amurka ta tura ƙarin sojoji 9,000 zuwa Gabas ta Tsakiya
Wasu jerin jiragen ruwa da ke kan hanyarsu ta zuwa Gabas ta Tsakiya na maƙare da jami’an jirgin ruwa fiye da 7,000 da sojojin ruwa na musamman 2,000, adadin da ya kara yawan sojojin ruwan Amurka a yankin.
Amurka ta tura ƙarin sojoji 9,000 zuwa Gabas ta Tsakiya
Jiragen ruwan da ke kan hanyarsu zuwa Gabas ta Tsakiya na ɗauke da sjami'an jiragen ruwa 7,000 da sojojin Marine 2,000.

Rundunar sojin Amurka ta tura ƙarin kusan dakarunta 9,000 zuwa Gabas ta Tsakiya a cikin wasu jiragen ruwa, a cewar wani jami’in Amurka.

Matakin na zuwa ne daidai lokacin da Shugaba Donald Trump ya sake gargaɗin cewa akwai yiwuwar kai sabbin hare-hare kan Iran.

Kazalika, a ranar Alhamis Trump ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa Iran na da alaƙa da matuƙin jirgin da ya daɓa wa kyaftin ɗinsa wuƙa tare da ƙoƙarin haddasa faɗuwar wani jirgin da ke kan hanyarsa ta zuwa Isra’ila a ranar Laraba.

Jiragen ruwan da ke kan hanyarsu zuwa Gabas ta Tsakiya na ɗauke da fiye da jami’ai 7,000 da sojojin ruwa 2,000.

Daga cikin tawagar jami’an da ke cikin jiragen akwai na rundunar USS Theodore Roosevelt, wadda kwanan nan ta tashi tare da jirgin yaƙi na USS Chosin, da kuma rundunar USS Makin Island, wadda ta ƙunshi jiragen saukar sojoji USS John P. Murtha da USS Anchorage.

Hakan na nufin manyan jiragen uku za su kasance a yankin da wuri kafin ƙarshen watan Oktoba, kamar yadda wani Jami’in Amurka wanda ya yi magana ba tare da bayyana sunansa ba saboda batun ya shafi ayyukan soji masu muhimmanci ya shaida wa The Associated Press.

Idan aka haɗa da jami’an tsaron da tuni suke Gabas ta Tsakiya, adadin jami’ai da kuma sojojin ruwan Amurka da ke yankin za su iya kai wa fiye da 20,000, tare da ɗaruruwan jiragen sama.

A watan Afrilu, an tura wa rundunar sojin ruwan tawagar jiragen kai hare-hare uku a Gabas ta Tsakiya karo na farko tun shekarar 2003.

A halin yanzu, jiragen USS George H.W. Bush da USS George Washington suna yankin, tare da rundunar USS Boxer.

Yawanci akan tura Jirgin Washington ne zuwa Tekun Pasifik ya yi aiki, amma sai a yanzu aka tura shi Gabas ta Tsakiya domin maye gurbin USS Abraham Lincoln, wanda ma’aikatansa suka shafe sama da kwanaki 260 a teku.

Damar Jam'iyyar Republican a zaben tsakiyar wa'adi a Amurka

A cikin wata hira da mujallar Time ta wallafa ranar Alhamis, Trump ya yi shelar kai ƙarin sabbin hare-hare, inda ya ce "akwai yiwuwar" ya kara tsananta kai hare-hare kan Iran bayan zaben da za a gudanar a Amurka a ranar 3 ga watan Nuwamba.

A yayin da aka matsa masa da tambayoyi, Trump ya ce ba zai iya yin karin bayani kan shirin dabarunsa ba.

"Ba zan iya gaya muku hakan ba saboda, kun sani, kuna tambaya ne kan yaushe zan kai harin bam?" in ji Trump.

Ya bayyana a hirar da aka yi da shi ranar Litinin cewa, ya yi watsi da sabon tayin yarjejeniyar tsagaita wuta daga Iran saboda "ƙa’idojin da ban amince da su ba shekara guda da ta wuce, ba zan amince da su ba a yanzuu."

Trump ya ba da misali da tayin da Iran ta yi na "buɗe Mashigar Hormuz" wata babbar hanyar jigilar makamashi a duniya, sai dai ya ce gaba ɗayan tayin "bai kai yadda ake so ba."

Yayin da aka tambaye shi ko yakin wanda jama'a ke kara nuna rashin goyon baya a kansa, zai iya shafar damar Jam'iyyar Republican a zaɓen watan Nuwamba, da farko Trump ya amsa da cewa, "Akwai yiwuwar hakan." Amma daga baya ya kara da cewa, "Ya kamata ya taimaka, saboda Iran ba za ta mallaki makamin nukiliya ba."

Shugaban ya ce "kashi 100 na mutane" sun ki amincewa Iran ta mallaki ikon kai harin nukiliya, "ciki har da al’ummar duniya."

"Don haka, idan aka kalle shi ta wannan fuskar, zai taimaka," in ji Trump. "Idan ba a kalle shi ta haka ba, zai iya haifar da matsala."