| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
1 minti karatu
Amurka ta ce China na shirin kai wa Iran makaman kare sararin samaniya – Rahoto
Wani rahoton kafar watsa labarai ta CNN ya ambato majiyoyi da ba a bayyana sunansu ba da kuma rahoton binciken sirri, wanda ya ce China na shirye-shiryen tura wa Iran wasu nau’ukan makamai masu linzami da ake harba su daga kafaɗa.
Amurka ta ce China na shirin kai wa Iran makaman kare sararin samaniya – Rahoto
Ginin Ma'aikatar Yaƙin Amurka Pentagon da ke Arlington, Virginia, wanda aka ɗauki hotonsa ranar 9 ga Oktoban 2020. / Reuters
 

Hukumar leƙen asiri ta Amurka ta nuna cewa China tana shirye-shiryen isar da sabbin makaman kariya daga hare-haren sama ga ƙasar Iran a ’yan makwanni masu zuwa, kamar yadda CNN ta ruwaito a ranar Juma’a, tana mai ambatar mutane uku da suke da masaniya kan lamarin.

CNN ta ce akwai alamu da ke nuna cewa China na ƙoƙarin tura kayayyakin ta wasu ƙasashe na daban domin ɓoye asalin inda makaman suka fito.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da Fadar White House da kuma ofishin jakadancin China da ke birnin Washington ba su mayar da martani ba dangane da buƙatar jin ta bakinsu da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nema.

Masu AlakaTRT Afrika - Makamai masu linzami na Iran na jarraba ƙarfin garkuwar makamai masu linzami a sararin samaniya


CNN ta bayyana cewa China tana shirye-shiryen tura makaman kariya daga hare-haren jiragen sama da ake ɗora su a kafaɗa waɗanda aka sani da MANPADs, tana mai ambatar majiyoyin da ba ta bayyana sunansu ba.

Gwamnatocin Amurka da Iran na shirin gudanar da wata babbar tattaunawa a ranar Asabar a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan, da nufin lalubo hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin da suka kwashe makwanni shida suna fafatawa.

MAJIYA:reuters
Rumbun Labarai
Abin da bayyanar ‘birnin makamai masu linzami’ na karkashin kasa na Iran ke nufi ga yankin
Daina taimaka wa sojojin Isra’ila ba ɗaya yake da kawo karshen haɗin baki da ita ba
Ƙawancen Saudiyya ya kakkabo makamai masu linzami huɗu da mayakan Houthi suka harba zuwa Riyadh
Sojojin Yemen sun kaddamar da hare-hare 875 kan Houthi, sun ce sun kashe 130 daga cikin mayakan
Ƙasashen Larabawa sun yi Allah wadai da yunƙurin mayaƙan Houthi na kai hari Madina
Dole ƙasashen Musulmai su tsaya tsayin daka kan ta’asar Isra’ila a Falasɗinu, in ji Turkiyya
Amurka ta kai hare-hare a Tsibirin Qeshm na Iran: Rahoto
Ƙawancen sojin Saudiyya ya harbo wani makami mai linzami da Houthi suka harba zuwa kudancin ƙasar
Iran ta ayyana rundunonin sojin ruwa da na saman Birtaniya a matsayin ƙungiyoyin ‘ta’addanci’
Isra’ila ta kai hare-hare fiye da 1,000 kan Syria cikin shekara biyu - Ministan Harkokin Waje
Khamenei ya umarci sojojin Iran su mayar da martani nan take idan Amurka ko Isra'ila suka kai hari
Pentagon ta ce yaƙin Iran ya laƙume dala biliyan 47
Jagoran adawa a Isra’ila ya nemi haɗin gwiwar jam’iyyun Larabawa domin kawar da Netanyahu daga mulki
Abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da zaben Isra’ila da me yake nufi ga Falasdinawa
Iran ta zargi Amurka da rashin gaskiya a tattaunawa, tana mai cewa tana ƙoƙarin tilasta mata buƙatu
Manyan jami’an Turkiyya, Saudiyya da Pakistan za su ziyarci Iran don tattauna batutuwan tsaro
Mayaƙan Houthi sun kai hari filin jiragen Riyadh, ƙawancen Saudiyya ta kai hari kan rokokin Sanaa
Netanyahu ya bayar da umarnin kulle yankin Yammacin Kogin Jordan da kuma rufe Hebron gaba ɗaya
Trump ya ce Amurka za ta iya kai wa Iran sabbin hare-hare
Turkiyya ta kawar da yunkurin jan kasar cikin yake-yaken yankin: Erdogan