| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Dukkan mutanen da ke ciki jirgin sojoji na Sudan sun mutu a hatsarin da ya yi
Daga cikin mamatan akwai matukin jirgi na soja Omran Mirghani, in ji ɗan'uwansa, shahararren ɗanjarida na Sudan Osman Mirghani, wanda ya nuna alhininsa a shafukan sada zumunta.
Dukkan mutanen da ke ciki jirgin sojoji na Sudan sun mutu a hatsarin da ya yi
Hatsarin jirage sun yawaita a Sudan. / AP
10 Disamba 2025

Wani jirgin saman sojin Sudan ya yi hatsari yayin da yake ƙoƙarin sauka a gabashin ƙasar, inda dukkan ma'aikatan jirgin suka rasa rayukansu, in ji jami'an soja a ranar Laraba, a sabon hatsarin jirgi a wannan ƙasar da rikici ya barke a cikinta.

An ce jirgin kaya na Ilyushin Il-76 ya samu matsalar na’ura yayin da yake ƙoƙarin sauka a ranar Talata a Filin Jirgin Saman Soja na Osman Digna a birnin da ke bakin teku na Port Sudan, in ji jami'ai biyu.

Sun ce ma'aikatan jirgin sun mutu amma ba su bayyana adadin mutanen da ke cikin jirgin ba. Jami'an sun yi magana bisa sharadi na rashin bayyana suna saboda ba a ba su izinin yi wa manema labarai bayani ba.

Daga cikin mamatan akwai matukin jirgi na soja Omran Mirghani, in ji ɗan'uwansa, shahararren ɗanjarida na Sudan Osman Mirghani, wanda ya nuna alhininsa a shafukan sada zumunta.

Faduwar jiragen sama ba sabon abu ba ne

Sojoji ba su yi sharhi kan hadarin ba.

Faduwar jiragen sama ba ta zama abin mamaki ba a Sudan, wadda ke da mummunan tarihin tsaron zirga-zirgar jiragen sama.

A watan Fabrairu, akalla mutane 46, ciki har da mata da yara, suka mutu lokacin da wani jirgin soja ya fadi a yankin da mutane suka cika a Omdurman, birnin makwabciyar babban birnin Khartoum.

Wannan hadari ya faru ne a yayin da sojoji ke ci gaba da yaƙi da ‘yan-awaren ƙungiyar Rapid Support Forces (RSF), wanda ya fara a Afrilu 2023 kan takaddama ta mulki tsakanin rundunar sojin ƙasa da RSF.

Rikicin ya kashe fiye da mutum 40,000 — adadin da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam ke ganin sun yi kaɗan ƙwarai.

Fadan ya lalata yankunan birane kuma an shaida ayyukan ƙiyayya, ciki har da fyaɗe a bainar jama'a da kashe farar hula da suka kai ga aikata laifukan yaƙi da laifukan ɗan adam, musamman a yankin yamma na Darfur, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam na ƙasa da ƙasa.

Yakin ya haifar da mafi muni na rikicin jinƙai a duniya kuma ya jefa wasu sassan ƙasar cikin yunwa.