| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
An kashe sojojin Bangladesh da ke aikin wanzar da zaman lafiya a sansanin MDD na Sudan: Bangladesh
Bangladesh tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi yawan sojojin da ke tawagar MDD da ke aikin wanzar da zaman lafiya kuma sojojinta sun daɗe a yankin Abyei na Sudan.
An kashe sojojin Bangladesh da ke aikin wanzar da zaman lafiya a sansanin MDD na Sudan: Bangladesh
Gwamnatin Sudan ta yi Allah wadai da harin da aka kai sansanin MDD. / AP / AP
3 awanni baya

An kashe sojoji shida na ƙasar Bangladesh, sannan aka jikkata soji takwas a wani “hari na ta’addanci” da aka kai a sansanin Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) da ke Sudan, a cewar rundunar sojin Bangladesh.

A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Asabar, rundunar sojin ta ce lamarin ya faru ne a yankin Abyei kuma yanzu haka ana ci gaba da gumurzu.

Kawo yanzu MDD ba ta ce komai game da wannan batu ba.

A wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Sudan ta yi Allah wadai da harin da aka kai sansanin MDD.

Gwamnatin soji ta Sudan da ke Port Sudan ta zargi dakarun Rapid Support Forces (RSF) da hannu a kai harin.

A sanarwar da Majalisar Ƙoli ta Sudan da ke ƙarƙashin Janar Abdel Fattah al Burhan ta bayyana hari a matsayin "mai matuƙar hatsari da ke yin ƙamari."

Yanki mai hatsari

Bangladesh tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi yawan sojoji a tawagar MDD da ke aikin wanzar da zaman lafiya kuma sojojinta sun daɗe a yankin Abyei na Sudan, yanki mai hatsari tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu.

An tura Dakarun Wucin-gadi na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya (UNISFA) zuwa Abyei ne a 2011.

Ƙasashen Sudan da Sudan ta Kudu ne suke gudanar da harkokin yankin Abyei mai arzikin man fetur, inda kowaccensu take iƙirarin mallakarsa kuma sun kwashe shekaru da dama suna taƙaddama a kansa.

A watan jiya aka sabunta aikin dakarun na wanzar da zaman lafiya.