WASANNI
2 minti karatu
Mohamed Salah ya cire Liverpool daga shafukansa na sada zumunta bayan wasansu da Frankfurt
Matakin da Salah ya ɗauka ya janyo ce-ce-ku-ce inda wasu ke cewa wannan wata alama ce ƙarara da ke nuna cewa ɗan wasan Masar ɗin yana son barin Anfield, lamarin da ke zuwa bayan ya fara kakar bana da rashin taɓuka wani abin azo a gani.
Mohamed Salah ya cire Liverpool daga shafukansa na sada zumunta bayan wasansu da Frankfurt
Wasu na ganin wannan matakin da Salah ya ɗauka na nufin yana son barin Anfield / Reuters
kwana ɗaya baya

Mo Salah ya ɗauki wani babban mataki kan shafukansa na sada zumunta bayan kocin Liverpool Arne Slot ya ajiye shi a benci a karawa mai muhimmanci da kulob ɗin ya yi da Eintracht Frankfurt a Gasar Zakarun Turai.

Matakin da Salah ya ɗauka ya janyo ce-ce-ku-ce inda wasu ke cewa wannan wata alama ce ƙarara da ke nuna cewa ɗan wasan Masar ɗin yana son barin Anfield, lamarin da ke zuwa bayan ya fara kakar bana da rashin taɓuka wani abin a zo a gani.

Matsalolin Mo yayin da kaka take tangal-tangal

Wannan kakar ta kasance mai cike da fargaba ga Salah, inda ingancin taka ledarsa ke raguwa kuma ake ganin raguwa a zura ƙwallonsa a raga da kuma damarmakin da yake  samarwa.

Gudunmawarsa wajen zura ƙwallo a raga ta ragu idan aka kwatanta da kakar da ta gabata.

 Kazalika ƙwarewarsa wajen yanka ya ragu yayin taɓa ƙwallonsa a gidan abokan gaba ya ragu, lamarin da ya nuna raguwa ƙwarewarsa.

Waɗannan na cikin dalilan da suka sa Slot ya ajiye shi a benci, wani mataki da ba a saba gani ba kan wani ɗan wasan da ake ganin shi ne ɗaya daga cikin ‘yan wasan Liverpool da aka fi yarda da su.

Wannan raguwar kaifin iya murza ledarsa ta ba da gudunmawa a rashin tabbas na wasannin da jagorar gasar Firimiyar take bugawa a kakar bana, inda wasu masharhanta da magoya bayan ƙungiyar ke ganin babu tabbas na ci gaba da kasancewarsa a cikin ‘yan wasan farko na ƙungiyar.

Zargin son kai

Duk da gagarumar nasarar da Liverpool da samu da ci 5-1 a Frankfurt, Salah bai taɓuka wani abin a zo a gani ba  bayan an saka shi a wasan minti 74 da fara wasa, kuma ya sha suka domin matakin buga ƙwallon da ya yi maimakon ya bai wa Florian Wirtz wanda ya samu damar zura ƙwallo.

Magoya bayan kulob ɗin da masharhanta sun bayyana wannan matakin a matsayin “son kai,” musamman yayin da Wirtz yake jiran ƙwallonsa na farko.
Magoya baya sun yi saurin tambaya game da abin da ya sa Salah ya yi irin wannan son kan.