AFIRKA
3 minti karatu
Dubban mutane sun tsere daga North Kordofan yayin da RSF ta zafafa kai hari a yankin Darfur na Sudan
Fiye da mutum 4,500 sun tsere daga birnin Bara, ciki har da mutum 1,900 waɗanda suka isa El Obeid, in ji wata ƙungiya ta ma'aikatan jinya ta cikin ƙasar.
Dubban mutane sun tsere daga North Kordofan yayin da RSF ta zafafa kai hari a yankin Darfur na Sudan
Fiye da mutum 36,000 sun tsere daga al-Fashir tun ranar Lahadi / Reuters
20 awanni baya

Fiye da mutum 4,500 sun tsere daga Jihar North Kordofan ta Sudan yayin da rundunar RSF  take ci gaba da kai hare-hare a yankin, kamar yadda ƙungiyar likitocin Sudan ta bayyana ranar Juma’a.

“Jihar North Kordofan tana fuskantar tserewa cikin gaggawa daga yankin Bara zuwa birnin El Obeid saboda taɓarɓarewar tsaro da kuma ci gaba da cin zarafin mutane da rundunar RSF ke yi wa fararen-hula,” in ji ƙungiyar ta ma’aikatan jinya a wani saƙon da ta wallafa a shafinta na X.

El-Obeid shi ne birni mai arzikin man fetur na Jihar North Kordofan, a yankin Kordofan mai maƙwabtaka da Darfur kuma wata muhimmiyar mahaɗa ce tsakanin Darfur da Khartoum.

“Rahotanni daga yankin na cewa adadin waɗanda aka raba da gidajensu ya zarce 4,500, ciki har da mutum 1,900 waɗanda suka isa birnin El Obeid, yayin da sauran suka kasance kan hanya a wani mawuyacin yanayi  kuma suna fuskantar tsananin ƙarancin abinci da ruwa da muhalli,” a cewar sanarwar.

Hukumar Hijira (IOM) ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta bayyana ranar Alhamis cewa  mutum 1,100 sun tsere daga Bara saboda taɓarɓarewar tsaro a yankin Darfur, lamarin da ya kawo adadin waɗanda aka raba da muhallansu cikin kwanaki huɗun da suka gabata zuwa 35,620.

Hukumomin Sudan sun ba da rahoton mace-mace da jikkata a wani harin jirgi maras matuƙa da rundunar RSF ta kai yankin Zareibat Sheikh El Borai a North Kordofan.

Sabunta yaƙi

Tun 15 ga watan Afrilu na shekarar 2023, sojin Sudan da rundunar RSF sun kasance cikin wani yaƙi wanda sa baki na ƙasa da ƙasa da na yanki ya gaza sasantawa. Rikicin ya kashe kimanin mutum 20,000 tare da mayar da mutum sama da miliyan 15 ‘yan gudun hijira, in ji MDD.

Hukumar lafiya ta MDD ta ba da rahoto ranar Alhamis cewa an kai samame asibiti na ƙarshe da ke aiki a birnin Al Fasher na Sudan,  kuma ana fargabar cewa an kashe ɗaruruwan mutane bayan RSF ta ƙwace birnin a wannan makon.

An katse hanyoyin sadarwa a cikin birnin kuma likitoci daga asibitin sun rasa intanet tun lokacin da RSF ta ƙwace sansanin sojin Sudan na ƙarshe a birnin ranar Lahadi, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito.

Ƙungiyoyin kare ‘yancin ɗan’adam sun daɗe da nuna fargabar cewa idan RSF ta karɓe iko da birnin Al Fasher da ke fama da tamowa za a iya fuskantar kisan ƙare-dangi kuma waɗanda suka tsere daga birnin sun ba da rahoton kashe-kashe na gilla.

‘Kisan ƙare-dangi’

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da jami’an Amurka  sun zargi RSF  da mayaƙa masu mara mata baya da kashe mutane da yawa a Darfur. Al Fasher muhimmin birni na ƙarshe da sojin Sudan ke riƙe da shi a yanki mai faɗi na yammacin Darfur yayin da take yaƙi da sojin a wani yaƙin da ya ɓarke a watan Afrilun shekarar 2023.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana a wata sanarwa ranar Laraba  cewa an sace likitoci huɗu da wani ma’aikacin jinya da wani ƙwararren mai haɗa magunguna daga asibitin Saudi.

Mazauna Al Fasher da likitoci da ma’aikatan agaji sun bayyana cewa rundunar RSF ta kasance tana kai hare-hare kan asibitoci a cikin Al Fasher a lokacin ƙawanyar, inda suke kai musu hare-haren roka da jirage maras matuƙa da kuma samame ta ƙafa.

A lokacin ƙawanyar, likitocin da suka tsaya a Al Fasher sun kasance suna yi wa mutane maganin cutar rashin abinci mai gina jiki da jin rauni da haihuwa a asibitin Saudiyya duk da ƙarancin kayayyakin aiki bayan an tsere daga sauran asibitocin saboda yawan fuskantar hare-hare.