Mutane da dama sun yi zanga-zanga a birnin New Delhi don neman gwamnati ta dauki mataki kan iska mai guba, yayin da wani hazo kairfi da ke dauke da ƙananan ƙwayoyin cuta masu hatsari ya mamaye babban birnin India.
Iyaye a ranar Lahadi a cikin dandazo sun dakko 'ya'yansu, waɗanda suka sanya abin rufe fuska da kuma daga alluna, tare da wani rubutu da ke cewa: "Ina kewar numfashi."
New Delhi, birnin da ke da yawan mazauna miliyan 30, yana cikin manyan biranen da suka fi gurɓatar iska a duniya.
Hazo mai sanyi yana rufe sararin samaniya a kowane lokacin hunturu, lokacin da iska mai sanyi ke taruwa da kusanto da gurɓatattun abubuwa zuwa kusa da ƙasa, inda hakan ke haifar da mummunan turnikewr hayaki skaamakon ƙona amfanin gona, masana'antu da cunkoson ababen hawa.
Matakin PM 2.5, wasu kananan halittu da ke janyo ciwon daji kuma suke iya shiga magudanar jini, a wasu lokutan suna daduwa har ninki 60, iyakar da MDD ta saka a kowace rana.
"A yau ina nan a matsayin uwa," in ji mai zanga-zanga Namrata Yadav, wacce ta zo tare da ɗanta.
"Ina nan ne saboda ba na son zama ‘yar gudun hijirar yanayi."
A ranar Lahadi, matakin PM 2.5 a fadin India Gate, wurin tunawa da yaƙi inda masu zanga-zanga suka taru, sun fi ninki 13 fiye da yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da shawarar kar ya wuce a kowace rana.
"Kowace shekara, labarin iri ɗaya ne, amma babu mafita," in ji Tanvi Kusum, wata lauya da ta ce ta zo ne saboda "tana takaicin me ke faruwa".
"Dole ne mu ƙara matsa lamba don gwamnati ta ɗauki lamarin da muhimmanci."
Matakin gwamnati
Matakan da gwamnati ta dauka sun gaza yin tasiri sosai wajen shawo kan matsalar.
Waɗannan matakai sun haɗa da takunkumi na ɗan lokaci kan jigilar mai da ake amfani da shi a sararin samaniya da kuma motocin ruwa da ke fesar da ruwa don share burbushin hazo daga iska.
"Gurbacewar muhalli na lalata rayuwarmu," in ji wata matashiya wacce ta yi iƙirarin cewa tana magana ne a madadin Delhi amma ta ƙi bayyana sunanta.
Wani bincike da aka yi a cibiyar ‘The Lancet Planetary Health’ a bara ya kiyasta rasa rayuka miliyan 3.8 a India da aka samu a tsakanin 2009 da 2019 suna da alaƙa da gurɓatar iska.
Hukumar Yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa gurɓatacciyar iska na jefa yara cikin hatsarin kamuwa da cututtukan numfashi masu tsanani.
Yayin da rana ta faɗi a sararin samaniyar da hayaƙi ya lulluɓe, taron masu zanga-zangar ya bayyana lamarin ma ya kara munana, kafin 'yan sanda su cusa wasu masu fafutuka a cikin motar bas, suna kwace allunansu da tutocinsu, suna jayayyar cewa ba su da izinin yin zanga-zanga a wajen.
Ɗaya daga allunan da rabinsa ya karye na cewa: "Ina son yin numfashi kawai."














