Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai fara ziyarar kwanaki uku a yankin Gulf a wannan mako, inda zai ziyarci Kuwait, Qatar da Oman daga ranar 21 zuwa 23 ga Oktoba, kamar yadda Fadar Shugaban Ƙasar Turkiyya ta sanar a ranar Litinin.
A cewar Shugaban Sadarwa na Fadar Shugaban Kasar Burhanettin Duran, a yayin ziyarar da za a kai bayan goron gayyata daga shugabannin kasashen yankin Gulf uku suka aiko - za a mayar da hankali kan ƙarfafa hadin gwiwar siyasa, tattalin arziki da tsaro, tare da daidaita matsaya kan mahimman batutuwan yankin da na ƙasa da ƙasa.
Ana sa ran Erdogan zai rattaba hannu kan wasu jerin yarjejeniyoyi da nufin faɗaɗa kasuwanci, zuba jari, da hadin gwiwar makamashi, in ji Duran a cikin wata sanarwa a shafin X.
Tafiyar tana jaddada yunƙurin da Ankara ke yi na ƙarfafa dangantakarta da ƙasashen yankin Gulf, biyo bayan kusantar juna albarkacin manyan yarjejeniyoyin tattalin arziƙi da kuma tattaunawa kan manyan tsare-tsare da aka yi.
Hakan na zuwa ne a yayin da Turkiyya ta ɗora kanta a matsayin babbar mai shiga tsakani kuma mai ƙarfin faɗa a ji a yankin, a lokacin da ake ci gaba da rikice-rikice da samun sauye-sauyen ƙawance a Gabas ta Tsakiya.
Shugaba Erdogan ya ziyarci yankin Gulf a karo na ƙarshe a watan Yulin 2023.