Sojojin Isra'ila a ranar Asabar sun bude wuta tare da harba hayaƙi mai sa hawaye kan manoma Falasdinawa a ƙauyen Kobar, da ke arewacin Ramallah a tsakiyar yankin Yammacin Kogin Urdun da aka mamaye, yayin da suke ƙoƙarin shiga gonakinsu domin girbin zaitun.
Wasu manoma daga Kobar sun yi ƙoƙarin isa gonakinsu da ke yammacin ƙauyen a lokacin da sojoji suka bude wuta a kansu, wanda ya tilasta musu janyewa, kamar yadda wani wakilin Anadolu ya ruwaito. Ba a samu rahoton ko wani ya jikkata ba.
“Sojojin mamayar (Isra’ila) sun hana manoma shiga gonakinsu da ke yammacin ƙauyen, musamman a yankunan Qanater da Daak, sannan suka buɗe wuta a kansu ba tare da jikkata kowa ba,” in ji wani manomi mai suna Fahd Abu al Hajj da Anadolu.
Ƙarin hare-haren ‘yan kama-wuri-zauna
Manoma sun tafi gonakinsu ne bisa hukuncin da Kotun Ƙolin Isra’ila ta yanke, wanda ya ba su izinin girbe zaitun a yankin da sojojin Isra’ila suka rufe a baya, in ji shi.
A cewar Abu al-Hajj, sojojin Isra’ila da Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna sun ɗade suna hana Falasdinawa shiga gonakinsu da ke kusa da ƙauyen da aka kafa ba bisa ƙa’ida ba da ke kusa da gidan Halamish, wanda aka gina a kan ƙasashen Kobar da wasu ƙauyuka makwabtaka.
A wani lamari daban da ya faru a rana ɗaya, wasu Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna da ke ɗauke da makamai ba bisa ƙa’ida ba sun kai hari kan masu girbin zaitun a garin Turmus Ayya da ke arewa maso gabashin Ramallah, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA ya ruwaito.
Haka kuma wani gungun ‘yan kama-wuri-zauna ya kai farmaki kan wasu iyalai a yayin da suke girbin zaitun a yankin al-Dilja da ke gabashin garin, suka fasa tagogin motarsu, sannan suka yi yunƙurin korar su daga wurin, amma iyalin sun ƙalubalanci maharan suka tilasta musu ficewa daga wurin.
Manoman Falasɗinu suna fuskantar hare-hare akai-akai daga sojojin Isra’ila da Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna a lokacin girbin zaitun na shekara-shekara, wanda sau da yawa ke hana su samun damar zuwa gonakinsu.