Hukumar kwastam ta Nijeriya reshen Jihar Adamawa ta sanar cewa jami’anta sun kama fatun jakuna 64 da aka yi yunƙurin fasa-ƙaurinsu zuwa ƙasar China.
Rahotannin daga ƙasar sun ambato kwanturolan hukumar reshen Jihar Adamawa, Garba Bashir yana cewa jami’an hukumar sun kama fatun jakunan ne ranar 30 ga watan Satumba na shekarar 2025, a bakin kogin Damare na Jihar Adamawa, inda masu fasa-ƙwauri suka ɓoye fatun kuma suke jiran faɗuwar rana domin su bi da su ta ruwa zuwa ƙasar Kamaru.
Hukumar ta kwastam ta kuma ƙwace man fetur da ƙwayoyi da aka yi yunƙrurin safarar su a kan iyakar ƙasar da Kamaru.
Kwaturolan ya ce kimar fatun jakunan da man fetur da ƙwayoyin ta kai naira miliyan 112.5.
Ya bayyana takaicinsa game da yadda ake fasa-ƙaurin dabbobi irin su jakuna, yana mai cewa hakan zai iya sawa a rasa jinsin waɗannan dabbobin baki ɗaya.
“Kashewa da kuma fitar da fatun jakuna ba bisa ƙa’ida ba ya ƙaru a faɗin Nijeriya saboda amfani da ake da su a magungunan gargajiya a ƙasar China,” kamar yadda ya bayyana wa manema labarai a Jihar Adamawa.
Ya bayyana cewa kamen ya faru ne cikin makonnin shida.
“Kayayyakin da aka ƙwace sun haɗa da: litar man fetur 20,600 da aka saka cikin jarka 824 wadda ko wannennsuu ke ɗaukar lita 25. Akwai katan 91 na ƙwayar tramadol samfurin 50mg wanda amfaninsa ya ƙare. Kazalika akwai katan 54 na sabulun ƙetare da kuma fatun jakuna 64 da aka yi yunƙurin fasa-ƙwaurin su zuwa ƙetare”, in ji shi.
Bashir ya bayyan cewa aikin hukumar kwastam ta Nijeriya ba kawai samar da kuɗaɗen shiga ba ne, har ma da kare lafiyar ‘yan ƙasar da tsaron ƙasa da kuma tattalin arziki.