Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) da ke Nijeriya ta amince da korar dalibai 171 bisa laifin gabatar da takardun shaidar shiga jami’a na bogi.
An cim ma wannan matsaya ne a taron majalisar dattawan jami’ar karo na 433, bayan rahoton da Kwamitin Majalisar kan Matsalolin Takardun Shiga Jami’a ya gabatar.
A cewar wata sanarwa da aka wallafa a cikin mujallar mako-mako ta jami’ar, an gano cewa ɗaliban da abin ya shafa sun gabatar da takardun bogi yayin neman gurbin karatu, wanda ya saɓa da dokokin jami’ar.
Jami’ar ta bayyana cewa wannan laifi ya saɓa wa Sashe na 20.7, Rukuni na A (vii) na Dokokin Jarabawa da Ka’idojin Ilimi na jami’ar, wanda ke tanadar da hukuncin kora ga irin wannan laifi.
BUK ta ƙara da cewa ɗaliban sun fito daga sassa da matakai daban-daban, inda ta jaddada cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin tsaftace bayanan karatu da kuma tabbatar da ingancin tsarin ilimi.
A wani ɓangare kuma, majalisar dattawan jami’ar ta amince da korar wani ɗalibi mai suna Yusuf Sani daga Sashen Injiniyan Gini, bisa zargin kai hari ga masu sa ido a lokacin jarabawa.
Jami’ar ta ce lamarin ya kawo cikas ga gudanar da jarabawar kuma ya saɓa wa dokokin ladabtar da ɗalibai. Haka kuma, mahukuntan jami’ar sun jaddada ƙudurinsu na tabbatar da gaskiya da nagarta a harkar ilimi, tare da gargaɗin cewa duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci mai tsauri.











