| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Shugabannin Turkiyya da Oman sun tattauna kan tashe-tashen hankula da ke ƙamari yayin yaƙin Iran
A wata tattaunawar waya, Recep Tayyip Erdogan ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran ka iya barazanar janyo wata "matsalar tsaro da ba a taɓa ganin irin ta ba" kuma ya jaddada buƙatar ci gaba da bin tafarkin diflomasiyya.
Shugabannin Turkiyya da Oman sun tattauna kan tashe-tashen hankula da ke ƙamari yayin yaƙin Iran
Erdogan na Turkiyya ya yi gargaɗi kan barazanar yanki mai ƙaruwa bayan hare-haren Iran, ya ce hare-hare kan Oman “abu ne da ba za a lamunta ba” / Reuters
19 Maris 2026

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Sultan ɗin Oman Sultan Haitham bin Tariq sun tattauna batutuwan dangantakar ƙasashen biyu tare da batutuwa na yanki a wata tattaunawar wayar tarho.

"Hare-hare kan Iran, wanda ramuwar gayyar Iran ta biyo bayanta kan ƙasashe maƙwabta na ‘yan uwa a yankin, sun saka yankin a barazanar matslaar tsaro da ba a taɓa ganin irinta ba," in ji Erdogan , yana mai jaddada cewa hare-hare kan Oman abubuwa ne da ba za a lamunta ba , in ji ofishin watsa labaran Turkiyya ranar Laraba.

Erdogan ya bayyana cewa Turkiyya ba ta yanke ƙauna ba kan ƙoƙarin dfilomasiyya, ciki har da shiga tsakani, duk da irin yanayin da ake ciki a yanzu, da kuma cewa za a ci gaba da irin wannan ƙoƙarin.

Shugaban ya kuma jaddada cewa yadda gwamnatin Benjamin Netanyahu ta Isra’ila ta hana Musulmai shiga masallacin Ƙudus na gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye “abu ne da ba za a lamunta ba” da kuma cewa Gaza na matuƙar buƙatar tallafin jinƙai.

Ya ƙara da cewa ƙoƙarin majalisar zaman lafiya da aka kafa kwanan nan ya kamata ya ci gaba da zummar samar da mafita ta ƙasashe biyu masu cin gashin kansu.

Erdogan ya kuma yi wa sultan ɗin fata na gari gabannin hutun Musulmi na ƙaramar sallah, wadda ke biyo bayan azumin watan Ramadan.