Rahotanni daga Nijeriya na cewa sojin ƙasa da na saman Nijeriya sun yi nasarar kashe ‘yanta’adda aƙalla 61 a garin Malam Fatori da ke jihar Borno a arewa maso gabashin ƙasar.
Wani rahoton da Zagazola Makama ya fitar wanda babban mai bai wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan dabaru da watsa labarai, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X, ya ce lamarin ya auku ne a lokacin ‘yanta’addan suka nemi kutsawa cikin sansanin soji a Malam Fatori da ke ƙaramar hukumar Abadam ta jihar Borno.
Rahoton ya ambato majiyoyin tsaro suna cewa ‘yanta’addan sun ƙaddamar da harin da sanyin safiyar Laraba ne inda suka nufi sansanin sojin da ƙafa kuma suka yi amfani da jirage mara matuƙa a wani yunƙuri na karya katangar sansanin sojin da ƙarfin hali.
Sai dai martani mai ƙarfi na haɗin gwiwa da dakarun ƙasa da na sama suka yi ya fi ƙarfin ‘yanta’addan.
Kazalika wata sanarwar da daraktan hulɗa da jama’a da watsa labarai na rundunar sojin saman Nijeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar kuma Usman Kuka Sheka tsohon kakakin sojin Nijeriya ya wallafa a shafinsa na Fabeook, ta tabbatar da aikin da sojin saman ta yi a Malam Fatori.
“Aikin na haɗin gwiwa ya yi nasarar hana masu tayar da ƙayar bayan karya katangun tsaro, lamarin da ya ƙarfafa ƙoƙarin da ake yi na daidaita lammura a garuruwan da ke kan iyakoki,“ in ji sanarwar.
Daga farko dai sanarwa ta bayyana cewa ɓangaren sojin sama na rundunar tsaro ta musamman ta Operation Hadin Kai ta yi nasarar fatattakar ‘yanta’adda a maɓuyarsu da ke Abirma, wata sananniyar dabar masu tayar da ƙayar baya a kudancin tafkin Chadi.
“An yi aikin ne bisa bayanan sirri da za a iya dogara kai da bayanan sa ido da da na bincike waɗanda suka tabbatar da kasancewa mayaƙan yanta’adda a matsugunin,” in ji sanarwar
“Bayanan sa ido da aka yi na tattara bayanai daga sama daga baya sun nuna kaikomon masu tayar da ƙayar baya kusa da gine ginen da aka ɓoye a ƙarƙashin shuke-shuke masu kauri, wata dabara da ake yawan amfani da ita domin kauce wa ganowa,” in ji shi.
Sanarwar ta ce rundunar sojin saman ƙasar ta ƙaddamar da hare-hare da makamai da ba sa kuskure kan wuraren da aka gano, lamarin da ya janyo lalata kayyakin ‘yanta’adda da yawa tare da katse ayyukansu a yankin .
“Bayanan farko na lalata ababen da yaƙi ya yi sun nuna cewa hare-haren sun rage ikon ‘yanta’addan na amfani da wurin domin ƙaddamar da hare-hare a faɗin yankin tafkin Chadi,” in ji sanarwar.














