Yankin Sahel na Afirka, wanda ya zama “inda ta’addanci ya fi ƙamari a duniya,” shi ne yake da kusan rabin mace-mace masu alaƙa da ta’addanci a shekara uku a jere, in ji rahoto kan ta’addanci a duniya da aka fitar ranar Alhamis.
Jadawalin ƙasashen, waɗanda cibiyar nazarin tattalin arziki da zaman lafiya ta yi, ya jera ƙasashe 163 bisa tasirin “ta’addanci” a kansu a cikin shekaru 13 kan alƙaluma na adadin hare-hare da mace-mace da raunuka da kuma adadin garkuwa da mutane.
Ta bayyana ta’addanci a matsayin “tsarin amfani da barazana ko kuma amfani da samame na ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba, ko domin taimaka wa ko kuma yin adawa da hukuma mai mulki.”
A shekarar 2024, fiye da rabin mace-mace 7,555 da aka samu sakamakon “ta’addanci” a faɗin duniya an same su ne a yankin Sahel, wani wuri da ya kama daga kudancin hamadar Sahara daga tekun Atalantika zuwa Bahar Ahmar.
Yanayin dai bai wani sauyawa ba a shekarar 2025, inda kusan rabin mace-mace 5,582 da aka laƙanta da “ta’addanci” suka faru a Sahel, duk da cewa adadin waɗanda lamarin ya rutsa da su a yankin ya sauka, in ji cibiyar nazarin da ke Australia.
“Yankin Sahel ya samu ƙaruwar mace-macen ta’addanci sau goma tun shekarar 2007”, lokacin da yake da kaso ɗaya cikin 100 na mace-mace masu alaƙa da ta’addanci a duniya.
“Tsakiyar inda ta’addanci ya fi ƙamari ta tashi daga Gabas Ta Tsakiya da Arewacin Afirka zuwa yankin Sahel da kuma Afirka kudu da Sahara,” in ji rahoton.
Burkina Faso ce ƙasar da lamarin ya fi shafa a shekaru biyu a jere, amma Pakistan ta wuce ta a shekarar 2025.

“Mace-mace daga ta’addanci a Pakistan a halin yanzu suna mataki mafi muni tun shekarar 2013, inda ƙasar ta samu mace-macen ta’addanci 1,139 da kuma aika-aika 1,045 da suka faru a shekarar 2025,” in ji rahoton.
“Wannan yana biyo bayan wani ƙarin aukuwar ta’addanci ne wanda a wani ɓangaren dawowar Taliban kan mulki a Afghanistan a shekarar 2021 ne ya janyo shi,” in ji rahoton, inda yake ishara ga ƙarin hare-haren ta’addanci na ƙungiyar Taliban ta Pakistan da kuma ƙungiyar BLA mai fafatukar neman ‘yancin ƙabilar Baloch, ƙungiyar ‘yan a-ware da ta fi ƙarfi .
Ƙungiyoyin JNIM da Daesh
Burkina Faso ta samu raguwar mace-mace mafi yawa a shekarar 2025 da kashi 45 cikin 100 daga shekarar da ta gabata, zuwa 846, in ji rahoton.
Abin da ya janyo mafi yawan wannan shi ne raguwa ta kashi 84 cikin 100 a mace-macen fararen-hula ba don ingantuwar tsaro tsaro.
Ƙungiya mai alaƙa da Al-Qaeda, wadda aka fi sani da suna JNIM, wadda ita ce mafi girman ƙungiyar ta’addanci da ke aika-aika a Burkina, ta sauya dabarunta zuwa kai hare-hare kan sojoji maimakon fararen-hula .
Nijar, wadda ta zo ta biyar a shekarar 2024, ta koma ta uku da ƙaruwar yawan aika-aikar “ta’addanci ” a shekarar 2025 kuma ta zarce Mali da Syria da mace-mace 703, wanda fiye da rabi na cikinsu fararen-hula ne.
Nijeriya ta koma ta huɗu a jerin ƙasashen, inda aka kashe mutum 750 a shekarar 2025, inda ya ƙaru da kashi 46 cikin 100 daga shekarar da ta gabata.
“Wannan shi ne adadin mace-mace mafi yawa tun shekarar 2020, lamarin da ya samo asali daga rashin kwanciyar hankali na cikin gida tare da rikicin da ake tsakanin ISWAP da Boko Haram,” in ji rahoton.
Mali ta samu raguwar mace-mace, kuma a halin yanzu ita ce ta biyar a jerin ƙasashen, inda aka kashe mutum 341 a shekarar da ta gabata idan aka kwatanta da da mutum 604 da aka kashe a shekarar 2024.
Rahoton ya alaƙanta yawancin hare-haren da ake kaiwa a yankin Sahel da ƙungiyoyin Daesh da JNIM.
Ya kuma bayyana faɗaɗawar ƙungiyoyin ta’addancin zuwa ƙasashen da ke gaɓar teku a Yammacin Afirka, musamman Benin, wadda ta tashi zuwa ta 19 a jerin ƙasashen daga ta 26 da take a da.
Sauran ƙungiyoyi, irin su ACLED, mai sa ido a kan mace-mace masu alaƙa da rikici a faɗin duniya, sun ba da rahoton adadin da suka fi haka yawa kan mace-mace masu alaƙa da ta’addanci a yankin Sahel.












