Iran ta ƙaddamar da jerin hare-hare na makamai masu linzami karo na biyar a cikin Isra’ila, a cewar kamfanin dillancin labaran Tasnim News Agency na ƙasar Iran.
An ji ƙarar jiniya a Birnin Ƙudus, Galilee da Haifa, kamar yadda kafar watsa labarai ta Channel 12 ta Isra’ila ta ruwaito.
Rundunar juyin juya hali ta Iran Revolutionary Guard Corps (IRGC) ta ce ta kai hare-hare ne a tsakiya da kudancin Isra’ila ciki har da Tel Aviv da sansanonin sojin Amurka da ke yankin inda ta ƙara da cewa dukkan hare-haren sun “samu cikakkiyar nasara, in ji Tasnim.
Rundunar IRGC ta ƙara da cewa yanzu haka tana ci gaba da kai hare-hare da manyan makamai masu linzami da kuma makamai masu cin gajeren zango.
Kafar watsa labarai ta Channel 12 ta ruwaito cewa tarkacen makamai masu linzami sun faɗa cikin Haifa Bay da birnin Shfar'am na arewacin Isra’ila.
Jaridar Yedioth Ahronoth da ke Isra’ila ta ruwaito cewa Iran ta harba makamai masu linzami masu ‘ya’ya cikin Isra’ila awa ɗaya da ta wuce.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Isra’ila, Magen David Adom, ya ce ba a samu rahoton mutuwa ba daga Haifa kuma babu wata babbar ɓarna da ta faru a Birnin Kudus da kewayensa.
Ya ƙara da cewa an tura tawagar domin kula da mutanen da suka jikkata sakamakon ruɗanin da suka shiga.












