Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Abdulƙadir, (Ƙaura) ya tabbatar da ƙarin masarautun gargajiya a fadin jihar a ranar Talata.
Gwamna Bala ya sanar da hakan ne bayan da kwamitin ƙirƙiro sabbin masarautu ya miƙa wa gwamnan rahotonsa da aka daɗe ana jira, wanda ya yi nazari kan samar da masarautu guda 13 da masarautar Zaar da kuma ƙarin hakimai 111 a faɗin jihar.
Tun mako biyu da suka wuce ne kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Hamza Koshe Akuyam ya miƙa wa gwmnan cikakken rahoton aikin da ya saka su.
Da yake jawabi bayan kammala sanar da tabbatar da ƙrin masarautun, Sanata Bala ya ce an yi hakan ne don bai wa yankuna da dama cin gashin kansu da kuma ba su dama don kawo ci gaba ga mutanensu da jin daɗi da walwalarsu.
“An yi musu daidai gwargwado, don ba za a iya yi wa kowa da kowa ba, duk da cewa kwamitin ya karɓi koke-koke da yawa, amma ba dama a ce kowa ya samu. Amma iya gwargwado dai mun yi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ba a ƙirƙiri sabbin masarutun don ba a son sarakunan yankan da ke kai ba. “mun yi ne saboda ko ina ma haka ake yi a duniya.
Ya ce irin waɗannan sarautu suna kawo ci aba wanda zai tilasta gwamnatin tarayya da sauran gwamnatoci su ga cewa sun yi wani abu na musamman na more rayuwa na al’ummar wadannan wurare, kamar masarautu da asibitoci.
Bala Ƙaura ya ce tun da aka yi jihar Bauchi ba a ƙara wasu masarutu ba a kan guda shidan da ake da su, “don haka mun yi ne da kyakkyawar niyya da kyakkyawar zuciya. Sannan yawan al’ummar jihar ya ƙaru sosai don haka ba daidai ba ne a cew ana zaune ba a samun ci gaba.
Sabbin masarautun sun haɗa da Burra da Damban, Darazo, Duguri, Gamawa, Giade, Toro, Warji, Ari, Jama’a, Lame, Bununu da kuma Lere.
Sai dai gwamnan bai faɗi matsayin kowace masarutar ba, wato daraja ta ɗaya ko ta biyu, kamar yadda kwamishin yaɗa labarai, Usman Shehu Zirami ya gaya wa TRT Afrika Hausa, yana mai cewa za a sanya hakan ne a cikin wasiƙar da za a bai wa sarakunan.
A nasa jawabin, shugaban majalisar dokokin Jihar Bauchi ya ce bayan gabatar musu da ƙudurin da gwmana ya yi, sai da suka yi zaman jin ra’ayoyin al;umma.
“Mu majalisa kamar yadda kuka sani muna wakiltar al’ummar jihar Bauchi ne, kuma dole su kawo mana koke-koke dole kuma mu saurare su. Kuma mun saurare su mun yi gyare-gyaren da ya dace,” in ji Abubakar Y. Suleiman.
Tun da fari, Akuyam ya ce, kwamitin masarautun wanda aka kafa ranar 4 ga watan Yulin 2025, ya samu buƙatu 196 daga al’ummomi daban-daban da ke neman a ba su sarautun da kuma yi garanbawul.
A cewarsa, daga cikin buƙatun da aka gabatar, 17 sun nemi a ƙirƙiri sabbin masarautu, 166 sun nemi a ba da sabbin hakimai, yayin da sauran suka nemi a ba da masarauta mai daraja ta uku.
Ya ce bayan yin nazari ne bisa tarihi da al’ada, sai aka samar da sabbin masarautu 13 da Masarautar Zaar da kuma hakimai 111.