GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Turkiyya, Masar, Qatar da Amurka sun sa hannu kan takardar yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza
An rattaba hannu kan wannan takarda ne a ranar Litinin yayin wani taron kasa da kasa da Masar ta shirya a wurin shakatawa na Bahar Maliya a Sharm el-Sheikh kan yarjejeniyar.
Turkiyya, Masar, Qatar da Amurka sun sa hannu kan takardar yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza
Turkiyya, Masar, Qatar da Amurka sun saka hannu kan yarjejeniyar Gaza / Reuters
6 awanni baya

Masar, Qatar da Turkiyya sun rattaba hannu tare da Shugaban Amurka Donald Trump kan wata takarda game da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

An rattaba hannu kan wannan takarda ne a ranar Litinin yayin wani taron kasa da kasa da Masar ta shirya a wurin shakatawa na Bahar Maliya a Sharm el-Sheikh kan yarjejeniyar.

Trump ya bayyana wannan rana a matsayin "babbar rana ga Gabas ta Tsakiya" yayin da shi da shugabannin yankin suka rattaba hannu kan wata sanarwa da aka tsara don tabbatar da tsagaita wuta a Gaza, bayan sa’o’i da Isra’ila da Hamas suka yi musayar fursunoni da wadanda aka yi garkuwa da su.

"Wannan babbar rana ce ga duniya, babbar rana ce ga Gabas ta Tsakiya," in ji Trump yayin da shugabannin duniya fiye da ashirin suka zauna don tattaunawa a taron.

"Takardar za ta fayyace dokoki da ka’idoji da sauran abubuwa da dama," in ji Trump kafin ya rattaba hannu, inda ya nanata sau biyu cewa "za ta tsaya daram."

Taron sake gina Gaza

Shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi ya bayyana cewa kasarsa za ta shirya wani taro kan sake gina Gaza bayan cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni da wadanda aka yi garkuwa da su.

"Masar za ta yi aiki tare da Amurka da hadin gwiwar abokan huldar mu a cikin kwanaki masu zuwa don kafa tubali na sake gina Gaza, kuma muna shirin shirya taron farfado da tattalin arziki, sake gina da ci gaba," in ji shi.

Sisi ya kara da cewa yarjejeniyar Gaza "ta rufe wani babi mai radadi a tarihin dan Adam kuma ta bude wani sabon zamani na zaman lafiya da kwanciyar hankali" ga Gabas ta Tsakiya.

Ya kuma kara da cewa wannan rana ta zama "rana mai tarihi" ga zaman lafiya wadda ta shimfida hanya don warware matsalar kasashe biyu.