An rantsar da Shugabar ƙasar Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan, a matsayin shugabar ƙasar a ranar Litinin a karon farko da aka zaɓe ta bayan ta yi nasara a zaɓen da ya haifar da zanga-zanga mai tsanani a faɗin ƙasar.
An ayyana Hassan, wadda ta hau mulki a shekarar 2021 bayan rasuwar tsohon shugabanta, a matsayin wadda ta lashe zaɓen makon da ya gabata da kashi 97.66% na ƙuri'un da aka kaɗa.
Sanye da jan mayafi da gilashi mai duhu, ta karbi rantsuwar kama aiki a wani biki da aka yi a sansanin sojoji a babban birnin Tanzania wato Dodoma.
Hassan, mai shekaru 65, ta tsaya takara ne kawai da 'yan takara daga ƙananan jam'iyyu bayan da aka hana manyan masu ƙalubalantarta daga manyan jam'iyyun adawa biyu shiga takarar.
Mummunar zanga-zanga ta barke a lokacin zaɓen na ranar Larabar da ta gabata, inda wasu masu zanga-zanga suka kunna wuta a gine-ginen gwamnati, 'yan sanda kuma suka harba hayaki mai sa hawaye da bindigogi, a cewar shaidu.
Babbar jam'iyyar adawa ta ce an kashe ɗaruruwan mutane a zanga-zangar, yayin da ofishin kare haƙƙin ɗan adam na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rahotanni masu inganci sun nuna cewa an kashe aƙalla mutane 10 a birane uku.
Gwamnati ta yi watsi da ikirarin ‘yan adawa game da adadin waɗanda suka mutu a rikicin inda ta ce “an kara gishiri a miya”.










