Mataimakin matuƙin jirgin flyDubai da ke kan hanyarsa zuwa Isra’ila ya sari matuƙin jirgin da gatari a wani yunƙuri na "ta’addanci", kamar yadda mai gabatar da ƙara na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya bayyana ranar Asabar, yayin da masu bincike ke aiki domin tabbatar da ko maharin ya yi aika-aikar ne shi kaɗai ko kuma yana da alaƙa da ƙungiyoyi masu tsattsarurar ra’ayi.
Mataimakin matuƙin jirgin flyDubai mai lamba FZ1073, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Isra’ila, ya kai hari kan matuƙin jirgin ne a cikin ɗakin matuƙin jirgin da wani gatari domin karɓe iko da jirgin, in ji babban lauyan gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) Hamad Saif Al Shamsi, kamar yadda kamfanin dillancin labaran WAM ya ruwaito.
Ana bincike domin tabbatar da yanayi da dalilai da ma sauran ababuwan da ke da alaƙa da lamarin, in ji shi.
Hukumomi suna kuma nazari kan hujjoji na bayyane da dijital a wani ɓangare na faɗaɗa bincike kan harin.
An bayyana Hamam al Hammami, ɗan ƙasar Oman, a matsayin wanda ake zargin, in ji mutum uku da ke da masaniya game da lamarin.
Majiyoyin, ciki har da wani na yankin Gulf da wani jami’in difilomasiyya, sun yi magana bisa sharaɗin sakaye sunayensu, tun da ba su da ikon zantawa da kafafa watsa labarai.
Fasinoji da ma’aikatan jirgin sun sa hannu kafin matuƙin jirgin ya ƙara jin rauni, in ji majiyoyin.
Masu bincike suna aiki domin tabbatar da ko al Hammami "ya yi aika-aikar shi kaɗai ne ko kuma yana da wata alaƙa da ɗaya daga cikin ƙungiyoyi masu tsattsaurar ra’ayi," in ji wani jami’in diflomasiyya.





















