Mai shari’a Anthony Onovo na babbar kotun tarayya da ke Enugu ranar Alhamis ya ba da umarnin cewa Gwamnatin Birtaniya ta biya diyyar fam miliyan 20 ga iyalan ko wane ɗaya daga cikin masu haƙar kwal 21 da masu mulkin mallaka suka kashe a jihar ta Enugu a shekarar 1949.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa kisan kiyashin ya faru ne a mahaƙar kwal ta Iva Valley Coal Mine a Enugu ranar 18 ga watan Nuwamba na shekarar 1949, wanda a wancan lokacin ya kasance babban birnin lardin gabashin Nijeriya da Birtaniya ke mulka.
Masu haƙar ma’adinan suna zanga-zanga kan mawuyacin yanayi na aiki da nuna wariyar launin fata wajen biyan albashi da kuma albashin da ba a biya ba, da suka ga cewa ba a biya musu buƙatunsu ba sai suka fara zanga-zanga ta “aiki maras yawa” kuma suka hana shugabannin mahaƙar kwal ɗin korarsu daga aiki.
Wannan ne ya sa sufiritandan na Birtaniya ya harbe masu haƙar kwal 21 kuma 51 suka jikkata.
Waɗanda lamarin ya rutsa da su sun haɗa da Sunday Anyasodo da Ani Oha da Andrew J. Obiekwe Okonkwo da Augustine Chiwetalu da Onoh Ugwu da Ngwu Offor da Ndunguba Eze da Okafor Agu da Livinus Ukachunwa da Jonathan Agu Ozoani da Moses Ikegbu Okoloha da kuma Chukwu Ugwu.
Har wa yau a cikinsu akwai Thomas Chukwu da Simon Nwachukwu da Agu Alo da Ogbonnia Ani Chima da Nnaji Nwachukwu da William Nwaku da James Onoh Ekeowa da Felix Nnaji dakuma Ani Nwaekwe.
Mai fafatukar kare haƙƙin bil’adama Greg Onoh, wanda ya shigar da ƙarar ya nemi gwamnatin Birtaniya ta yarda cewa lamarin ya faru sannan ta nemi gafara tare da biyan cikakkiyar diyya kan rayukan da aka rasa ga iyalan mamatan.
Waɗanda aka kai ƙara sun haɗa da sakataren harkokin wajen ƙasashen renon Ingila da aikace-aikacen ci-gaba da Gwamnatin Birtaniya da kuma Gwamnatin Nijeriya.
Kazalika akwai Antony Janar na tarayya da kuma shugaban ƙungiyar ƙasashe renon Ingila da kuma Gwamnatin Birtaniya na cikin waɗanda aka kai ƙarar.
NAN ya ba da rahoton cewa babu lauyan da ya wakilci waɗanda ake ƙara na ɗaya da na biyu da huɗu da na biyar da kuma shida.
Da yake yanke hukuncin, Alƙali Onovo ya bayyana kisan kiyashin a matsayin wanda ya saɓa wa doka da kuma kisan gillan da ya tauye ‘yancin gudanar da rayuwa, inda ya ɗora alhakin laifin kan gwamnatin mulkin mallaka ta Birtaniya kuma ya ba da umarnin biyan diyya mai yawa da neman gafara a hukumance da kuma mataki na diflomasiyya.
Alƙalin ya ce dole a ɗoura wa gwamnatin Birtaniya alhakin laifin kuma dole ta biya diyya ga iyalan masu haƙar kwal ɗin 21.
“Waɗannan masu haƙar kwal mara kariya sun kasance suna neman ingantaccen yanayi na aiki ne, ba su ɗauki wani mataki na tashin hankali ba ga hukumomi, amma an harbe su kuma an kashe su,” in ji alƙalin.














