Gwamnatin ƙasar Ghana ta ƙara farashin koko zuwa GH₵5,800 kan ko wane tan bayan zaman gaggawa da kwamitin da ke sanya farashin ga noman kokon ya yi.
Ministan Kuɗi, Cassin ƙasar Cassiel Ato Forson, wanda ya bayyana matsayin da kwamitin ya ɗauka, ya ce sabon farashin na nufin za a riƙa sayen kowane buhun koko mai nauyin kilogiran 64 kan GH₵3,625.
Kamfanin dillancin labaran Ghana ya ruwaito cewa wannan na nufin an samu ƙarin GH₵4,00 kan ko wane buhun koko.
A watan Agusta na wannan shekarar gwamnatin ƙasar ta ƙayyade farashin da manoma za su sayar da koko a kakar 2025/2026 kan GH₵51,660 kan ko wane tan na koko.
Sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar Jumma’a 3 ga watan Oktoban shekarar 2025.
Dakta Forson ya bayyana cewa farashin na baya ya kasance bisa hasashen da aka yi ne kan farashin koko a duniya da kuma farashin a kasuwar musayar kuɗaɗe ta ƙasa da ƙasa.
“Daga bisani, mun ga wasu sauye-sauye, saboda haka yana da muhimmanci mu sake sauya farashin ga manoma, “ in ji Dakta Forson.
Ya ce hukumar kula da koko ta COCOBOD za ta ci gaba da ɗaukar matakai domin tallafa wa noman koko da kuma inganta rayuwar manoma.
Ya ce COCOBOD za ta ƙara ƙaimi wajen bayar da takin zamani na koko a kyauta (na ruwa da na ƙwaya) da maganin kashe ƙwari da injinan feshi kyauta da sauransu.
Kazalika ya ce hukumar COCOBOD na kan hanyarta ta samar da sabon tsarin karatu kyauta ga ya’yan manoma koko a shekarar karatu ta shekarar 2025/20-26.
Ya ce gwamnatin ta jajirce wajen tallafa wa hukumar koko ta Ghana wajen gina fannin ta yadda duk masu ruwa da tsaki za su amfana.