Manufar Amurka ta tasa ƙeyar ’yan ci-rani zuwa ƙasashen Afirka da ba ƙasashensu na asali ba ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa, kuma tana amfani da wahala wajen hana mutane yin ƙaura, a cewar ƙungiyar Human Rights Watch (HRW).
Bayan Shugaba Donald Trump ya koma fadar White House a watan Janairun 2025, gwamnatinsa ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da ƙasashen Latin Amurka, Afirka da yankin Pacific domin karɓar ’yan ci-ranin da ba za a iya mayar da su ƙasashensu na asali ba.
Tun daga wannan lokacin, Amurka ta tasa ƙeyar fiye da mutane 500 zuwa ƙasashen Afirka da ba ƙasashensu na asali ba, kamar yadda alkaluman Hukumar Kula da Shige da Fice da Kwastam ta Amurka (ICE) da HRW ta duba suka nuna.
Wani bincike da ƙungiyar kare ’yancin manema labarai, Forbidden Stories, ta wallafa ya kiyasta cewa kusan mutane 25,000 ne aka tasa ƙeyarsu zuwa ƙasashe daban-daban na duniya a ƙarƙashin wannan shiri.
HRW ta ce manufar “ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa na kare haƙƙin bil’adama, kuma an tsara ta ne domin amfani da wahalar bil’adama wajen hana ci-rani.”
Ƙungiyar ta kuma ambato wani jami’in Amurka da ba a bayyana sunansa ba, wanda ya shaida wa wani kwamitin bincike na Majalisar Dattawan Amurka cewa, “ga ƙasashe irin su Palau da Eswatini, bayanin shi ne gwamnatin za ta iya barazana ga mutane cewa za a sake su ne a cikin daji. Abin da ake son yi shi ne a razar da mutane.”
HRW ta ce ta tattauna da mutane 24 da aka tasa ƙeyarsu zuwa ƙasashen Afirka da ba ƙasashensu na asali ba, ciki har da Kamaru, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, Equatorial Guinea, Eswatini da Sudan ta Kudu.
Sun bayyana yadda aka ɗaure su da sarƙoƙi yayin tafiyar jirgin da ta kai tsawon sa’o’i 18, ba tare da sanin inda ake kai su ba.
HRW ta ce da yawa daga cikin yarjejeniyoyin da aka kulla tsakanin Amurka da waɗannan ƙasashe har yanzu ba a bayyana su ga jama’a ba.
Wani binciken AFP da aka gudanar a farkon shekarar 2026 ya nuna irin matsin lambar da Washington ta yi wa wasu ƙasashen Afirka, ciki har da barazanar kakaba musu haraji, dakatar da bayar da biza ko rage tallafin da suke samu, domin tilasta musu karɓar mutanen da Amurka ta tasa ƙeyarsu.
Burundi, ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fama da talauci a duniya, ta bayyana a farkon wannan watan cewa ta amince da karɓar mutanen da Amurka ta tasa ƙeyarsu, inda ta zama ƙasa ta 15 a Afirka da ta kammala irin wannan yarjejeniya da Washington.





















