Likitocin Sudan sun ba da rahoton cewa dakarun RSF sun ci zarafin mata 19, ciki har da mata biyu masu ciki a arewacin Sudan.
Ƙungiyar likitocin Sudan ta bayyana a cikin wata sanarwa a shafin X na Amurka cewa an yi wa mata fyaɗe yayin da suke tserewa daga birnin Al Fasher, babban birnin Jihar North Darfur, wanda a yanzu yake ƙarƙashin ikon RSF, zuwa Al Dabbah a Jihar da ke arewacin ƙasar.
“Biyu daga cikin waɗanda aka yi wa cin zarafi suna da juna biyu kuma a halin yanzu suna karɓar magani na musamman a ƙarƙashin kulawar ma’aikatan jinya na cikin gida,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ƙungiyar ta yi Allah wadai da “fyaɗe irin na gungun maza da RSF ke aikatawa ga mata da ke tserewa daga bala’in Al Fasher,” tana mai jaddada cewa far ma mata kai-tsaye tsabagen keta dokokin ƙasa da ƙasa ne.
Ta yi kira ga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama su rubuta zaluncin da RSF take aikatawa kan fararen-hula ta hanyar tura masu bincike da ke zaman kansu domin kare mata da yara wuraren da aka kori mutane da kuma hanyoyi na tafiya da kuma samar da amintattun wurare ga mata da ƙananan yara.
Ranar 26 ga watan Oktoba ne mayaƙan RSF suka ƙwace Al Fasher kuma an zarge su da aikata kisan kiyashi kan fararen-hula, inda suka raba fiye da mutum 40,000 da gidajensu, in ji rahotanni na cikin gida da na ƙetare.
Dakarun RSF ne ke da iko kan dukkan jihohi biyar na yankin Darfur daga cikin jihohi 18 na ƙasar, yayin da sojin ƙasar ke da iko da yawancin sauran jihohi 13 na ƙasar ciki har da babban birnin ƙasar Khartoum.
Yaƙin basasa tsakanin sojin Sudan da rundunar RSF, wanda aka fara a watan Afrilun shekarar 2023, ya kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da gidajensu.


















