| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Tsawa ta kashe fiye da mutum 12 a Malawi sakamakon mamakon ruwan sama da walkiya
Wilson Moleni, kwamishina na Ma'aikatar Kula da Harkokin Bala'i ta gwamnati (DoDMA), ya shaida wa 'yanjarida a babban birnin, Lilongwe, cewa mace-macen da lalacewar abubuwan more rayuwa sun faru ne a sassa daban-daban na ƙasar.
Tsawa ta kashe fiye da mutum 12 a Malawi sakamakon mamakon ruwan sama da walkiya
Ana fuskantar ruwan sama mai karfi tare da walƙiya a faɗin Malawi. / AA
12 awanni baya

Tsawa ta kashe mutane 14 a Malawi cikin makonni biyu da suka gabata, yayin da gidaje 8,000 suka lalace sakamakon mamakon ruwan sama, in ji jami'an kula da bala'i a ranar Jumma'a.

Wilson Moleni, kwamishina na Ma'aikatar Kula da Harkokin Bala'i ta gwamnati (DoDMA), ya shaida wa 'yanjarida a babban birnin, Lilongwe, cewa mace-macen da lalacewar abubuwan more rayuwa sun faru ne a sassa daban-daban na ƙasar.

“Amma tun da ƙasar na ci gaba da samun ruwan sama mai ƙarfi, akwai yiyuwar adadin mamatan zai ƙaru da lokaci,” in ji Moleni a ranar Jumma'a.

Ya ce ƙungiyarsa na aiki "ba gajiya" don samar da tallafin jinƙai ga waɗanda ruwan sama ya sanya su rasa matsuguni a faɗin ƙasar.

“Muna roƙon al'umma da su ɗauki matakan kariya yayin da ruwan sama ke ci gaba, domin hakan na iya hana ƙarin asarar rayuka,” ya ce.

A bara, a wannan lokaci, aƙalla mutane takwas ne suka mutu, kuma iyalai 10,000 sun rasa matsuguni sakamakon ruwan sama mai ƙarfi.

A shekarar 2023, guguwa mai suna Cyclone Freddy ta kashe dubban mutane a yankin kudu na ƙasar kuma ta tilasta miliyoyin mutane yin hijira.

Ƙasar ba ta sake murmurewa daga ɓarnar tattalin arzikin da guguwar ta janyo ba.

A cikin shekaru biyu da suka gabata, ƙasar na fama da matsanancin ƙarancin abinci.

A watan da ya gabata, Shugaba Arthur Peter Mutharika ya ayyana halin bala'i na ƙasa a dukkan gundumomi 26 na ƙasar kuma ya nemi gaggawar tallafin jinƙai, amma a cewar DoDMA, har yanzu akwai "babban gibin kudi" don kauce wa rikicin jinƙai.