| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Sojojin Sudan sun ƙwace wani muhimmin gari a Arewacin Kordofan bayan arangama da RSF
Ƙungiyar Dar Hamar Emergency Response Room ta yankin ita ma ta sanar da cewa sojojin sun kwace garin.
Sojojin Sudan sun ƙwace wani muhimmin gari a Arewacin Kordofan bayan arangama da RSF
Sojojin Sudan sun ƙwace wani muhimmin gari a Arewacin Kordofan bayan arangama da RSF
 

Rundunar sojin Sudan ta ce ta karɓi cikakken iko da garin Al-Mazroub da ke jihar North Kordofan a ranar Juma’a, bayan kazamin fada da rundunar RSF mai rajin kare kai.

Kakakin rundunar musamman ta sojin Sudan, Mohamed Deidan, ya tabbatar wa Anadolu da cewa sojojin sun karɓi cikakken iko da garin bayan arangama da RSF.

Deidan ya bayyana ƙwace garin a matsayin wani muhimmin mataki a ƙoƙarin sojojin na katse hanyoyin samar da kayayyaki ga RSF, yana mai cewa Al-Mazroub na da muhimmiyar alaƙa tsakanin jihohin North Kordofan da West Kordofan.

Ya ce nasarar ta sauya yanayin yaƙin da ake yi a yankin Kordofan.

Al-Mazroub yana arewa maso yammacin North Kordofan, kimanin kilomita 90 daga yammacin Bara.

Ƙungiyar Dar Hamar Emergency Response Room ta yankin ita ma ta sanar da cewa sojojin sun kwace garin.

Kakakinta, Azzam Hamed, ya shaida wa Anadolu cewa kwace Al-Mazroub “ya buɗe wa sojojin hanya zuwa jihar West Kordofan.”

Wasu sojojin Sudan sun wallafa faifan bidiyo a kafafen sada zumunta suna sanar da cewa sun karɓi iko da garin.

A ranar 26 ga Satumba, sojojin Sudan sun sanar da kwace yankin Um Sharo da ke North Kordofan, kwana guda bayan sun bayyana cewa sun karɓi iko da Sodari, tare da cewa sun yi wa RSF asara mai yawa.

A baya-bayan nan, sojojin sun ce sun samu gagarumar nasara a sassa da dama na North Kordofan bayan arangama da RSF, inda suka sanar da kwace iko da yankuna 11 a jihar.

Jihohin North Kordofan, West Kordofan da South Kordofan sun kasance fagen arangama tsakanin sojojin Sudan da RSF tun ranar 25 ga Oktoban bara.

Sudan na fama da yaƙi tsakanin sojojin ƙasar da rundunar RSF tun watan Afrilun 2023. Alkaluman Majalisar Ɗinkin Duniya da wasu ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun nuna cewa rikicin ya kashe dubban mutane tare da raba kusan miliyan 13 da muhallansu.

Rumbun Labarai
Tsawatarwar diflomasiyya da aka yi wa jakadan Nijeriya abu ne da aka gama batunsa: Afirka ta Kudu
Ghana ta ba da shawarar fara amfani da kuɗin ECO a matakai tsakanin ƙasashen ECOWAS da suka shirya
Sojojin Sudan sun sami ƙarin wurare a jihar West Kordofan yayin da mayaƙan RSF ke ja da baya
Shugaba Tiani na Nijar ya nada Aboubacar Issaka a matsayin sabon shugaban ’yansandan kasar
Ghana na samun tan 62 na sinadarin mercury a kowace shekara ta hanyoyin da ba su dace ba
Rundunar tsaron Nijar ta ƙwace makamai da ake zargin ana shirin kai wa Boko Haram a Diffa
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da gyaɗa zuwa ƙasashen waje
Sudan ta Kudu ta sake dage babban zaben kasar zuwa ranar 11 ga Fabrairun 2027
Amurka za ta sa ido sosai kan zaben shugaban kasar Nijeriya na watan Janairu - Jami’i
An kashe fararen-hula akalla 37 a wani harin kwanton-ɓauna a yammacin Jamhuriyar Nijar
An kashe aƙalla mutum 10 yayin da dakarun tsaron Guinea suka yi arangama da masu haƙar zinare
Ghana za ta kashe dala miliyan 200 kan shirya wa gina tashar makamashin nukiliya
Ghana ta kaddamar da sabuwar takardar kudi ta Cedi
Burhan na Sudan ya buƙaci a cire siyasa a rabon tallafin yaƙi da sauyin yanayi ga ƙasashe mara ƙarfi
Greenpeace ta gargaɗi Ghana kan barazanar shara sakamakon shigo da tsofaffin tufafi miliyan 1 a mako
Yadda El Niño ke sake haifar da ɓarkewar cutar Zazzaɓin Rift Valley a Gabashin Afirka
BAMEX 2026: An fara baje-kolin fasahar tsaro ta ƙasa da ƙasa a Mali
Kotu a DR Congo ta yanke wa sojoji 66 hukuncin kisa saboda 'ja da baya a fagen daga'
Kwale-kwale dauke da ‘yan ci-rani ya kife a kusa da Senegal, mutum 21 sun rasu, in ji hukumomi
An yanke wa jagoran ƙungiyar asiri a Kenya hukuncin ɗaurin shekara 200 kan kisan yara 190