Shugaban ƙasar Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya karɓi baƙuncin shugaban ƙaramar hukumar Bilma da mutanensa da aka kuɓutar daga hannun masu garkuwa da mutane bayan sun shafe watanni16.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewa shugaban ƙasar ya gana da shugaban ƙaramar hukumar ne ranar Talata.
Sakatare janar na ma’aikatar tsaron ƙasar kuma babban kwamishinan ‘yan sanda, Ayouba Abdourahamane, ya bayyana cewa shugaban ƙaramar hukumar ta Bilma da mutanensa sun samu lambar girmamawa daga hannun ministan tsaron cikin gidan ƙasar, Manjo Janar Mohamed Toumba.

Kuma bayan wannan girmamawar ce "shugaban ƙasar ya nemi ganinsu domin ba su shawarwari da kuma sanin irin halin da suka kasance a lokacin da suke hannun masu garkuwa da mutane," in ji shi, yana mai cewa "shugaban ƙaramar hukumar Bilma ya bayyana mana duk abubuwan da suka faru."
Babban jami’in na ma’aikatar tsaron cikin gidan ya tabbatar da cewa za su ɗauki dukkan matakan da suka kamata domin tabbatar da cewa irin wannan matsalar ba ta sake faruwa ba.











