| Hausa
Ra'ayi
KASUWANCI
4 minti karatu
Afrika na amfani da tagomashin da zinari yake samu don ƙara ƙarfin arziƙinta
Afirka za ta iya ribatar wannan lokaci da duniya take fuskantar rashin tabbas a tushen cinikayya, don gina turbar bunƙasar arziƙi da zaman-kanta. Yayin da duniya ke neman mafaka a hada-hadar zinari, ita kuma Afirka ta nemi madogara kansa.
Afrika na amfani da tagomashin da zinari yake samu don ƙara ƙarfin arziƙinta
Afirka tana da sama da kashi 40% na ajiyar zinari na duniya, amma har yanzu tana makale cikin mawuyacin hali a matakin fitar da albarkatun kasa na sarkar daraja. Hoto / Reuters
27 Janairu 2026

Yayin da duniya ke shaida ƙaruwar tunzurin siyasar duniya, daga Gabashin Turai zuwa Tekun Kudancin China, wata al'ada tana sake maimaituwa, wato rububin tara zinariya.

Wannan ƙarfe mai tarihi na tsawon zamuna, ba kawai hajar kasuwanci ba ce, wata kadara ce mai gagarumar mafaka ce mai adana kimar kuɗi.

Hawan farashin da aka gani kwanan nan a kimar zinari, yana zama wani ma’auni na kai-tsaye na fargabar da duniya ke ciki, wanda ke nuna raunin aminci kan tsarin duniya.

Ko da yake wannan buƙata da rikici ke haifarwa ta nuna matsayi na har abada da zinari ke da shi. Yanayin yau wata dama ce mai muhimmanci ga Afirka, amma wata wadda dama ake watsi da ita, saboda matsayin nahiyar na yalwar arziƙi.

Ya wajaba mu sauya daga zama wajen haƙar ma’adanai na duniya, don zamowa nahiya mai 'yancin hada-hadar kuɗinta, ta amfani da wannan lokaci don saka ɗambar wannan sauye-sauyen.

Mafi ingancin ma'ajiyar kima

Mutane na komawa ga zinari a lokutan rikici saboda dalilai masu zurfi. Shi ne ma’adanar kadara ta ƙarshe, wadda ke taskace kima a fili, wadda ba a iya rage darajarta ta hanyar taɓarɓarewar harkokin manyan bankunan ƙasa sakamakon rikicin siyasa a duniya.

Idan kuɗaɗe suka samu rashin tabbas, kuma ƙawance ya sassauya, zinari kan zama daban, saboda yakan ba da sauƙin maidawa kuɗi da kuma karɓuwa ko'ina a duniya.

Baya ga tattalin arziƙi kaɗai, zinari na da kima a al’adance musamman a ƙasashen Afirka, Asiya, da Gabas ta Tsakiya, inda yake ba da tsaro da kima a al’umma tsawon zamuna.

Wannan buƙatar da ta ƙazance, ba wai ta ɗokin da aka gina kan hasashe ba ce; wata dabarar sauya lissafi ce ta ɗaiɗaikun mutane da ƙasashe, waɗanda ke neman daidaito a yanayin duniya mai rashin tabbas.

Manyan bankunan duniya, musamman a ƙasashen kudancin duniya, suna jagorantar wannan yunƙuri, suna tara zinari don rage dogaro kan taskar ajiyar dalar Amurka, da kuma ƙarfafa 'yancin su na hada-hadar kuɗi.

Ga Afirka, wannan sauyin matsayi na duniya wani kiran gaggawa ne. Nahiyar tana da sama da kashi 40% na taskar zinari na duniya, amma har yanzu tana cikin haɗarin kasancewa a matakin fitar da albarkatun ƙasa da ba a sarrafawa ba.

Wannan yunƙuri da rikici ke haifarwa dole ne ya zama makamashin gagarumin canji. Abin da ya zama wajibi shi ne mu riƙe wannan arziƙi a cikin gida ta hanyar ƙara darajar albarkatun mu.

Wannan na nufin ginawa da faɗaɗa matatun gida, kafa maƙerar samar da sulalla masu ikon mallakar ƙasa don samar da bullion da tsabar kuɗi da ke ɗauke da sunan nahiyar, da haɓaka masana'antar ƙera kayan ado na zinari.

Kowane giram na zinari da aka tace, aka ƙera, kuma aka sayar a cikin Afirka yana samar da ayyukan-yi, yana riƙe ƙima, kuma yana gina ƙarfin masana'antu. Yana mayar da ɗanyun albarkatu zuwa sarrafaffen kaya mai ɗauke da alamar Afirka.

Musayar zinari a yanki

Haka kuma, dole mu jagoranci ƙirkire-ƙirkire na hada-hadar kuɗi da aka gina a kan arziƙin zinarinmu. Mu ƙaddara samar da wani nau’in kadarar kuɗi ta yankin Afirka da aka jingina kan zinari, a wani haɗin-gwiwa da zai iya tallafawa ayyukan more rayuwa ko daidaita darajar kuɗaɗenmu.

Ta hanyar kafa tsarin musayar zinari ta yanki, za mu iya sauƙaƙa ciniki kan kwangilolin zinari, da aka kimanta bisa kuɗaɗen gida, rage dogaro da dalar Amurka, da gina tsarin kuɗi mai juriya.

Wannan ba ja-da-baya daga harkokin kuɗi na duniya ba ne, sai dai wata mu'amala ce mai hikima da za ta ba mu damar inganta 'yancin-kanmu.

A lokaci guda, dole ne mu tsara kuma mu ƙarfafa sashen haƙar ma'adinai na gargajiya, wanda ke ba da gudummawa mai yawa ga ƙarfin samarwarmu.

Ba wa ma'adanai damar samun kasuwanni masu adalci, fasahohi mafi inganci, da yanayin aiki mai tsaro zai haɗa su cikin tattalin tsararren tattalin arziƙin, ya ƙara kuɗaɗen shiga ga ƙasa, kuma ya tabbatar da kimar zinarinmu yayin da ake samun tagomashinsa a duniya.

Gaggawar duniya zuwa tara zinari a lokutan tsoro, abu ne da ya kasance a tarihi. Amsar Afirka, duk da haka, ba dole ta kasance mara karsashi ba.

Muna da arziƙin; abin da muke buƙata yanzu shi ne hangen nesa mai ƙarfi da haɗin-gwiwar siyasa don sake tsara dukkanin matakin kima.

Ta yin haka, za mu iya mayar da wannan lokaci na rashin tabbas na duniya zuwa ginin wadata mai ɗorewa, kwanciyar hankali, da 'yancin kai na hada-hadar kuɗi ga Afirka. A bar duniya ta nemi mafaka a zinariya; a bar Afirka ta gina makomarta da kanta.

Marubucin, Kennedy Chileshe, shi ne Daraktan Zartarwa na Jubilee Leaders Network a Zambia, kuma yana mayar da hankali kan batun Jagoranci da Gwamnati.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba lallai su nuna ra'ayoyi, hangen nesa, ko manufofin editan TRT Afrika ba.