Wani ɗan Nijeriya, Fado the Great yana ƙoƙarin maido da tashen wasan tsafi
King Fad na son sauya fasalin alaƙar Nijeriya da fasahohin gwaninta. / Others
Wani ɗan Nijeriya, Fado the Great yana ƙoƙarin maido da tashen wasan tsafi
Ibitoye King Fad ya ɗauki ɗambar kwashe awanni 50 yana wasan tsafi ba tsayawa a Lagos, da niyyar bayyana hazaƙar wata fasaha da ake yawan yi wa mummunar fahimta.
2 Disamba 2025

Daga Charles Mgbolu

A wani dandali da ke birnin Lagos na Nijeriya, Ibitoye King Fad, wanda aka fi sani da “Fado the Great”, ya saka tufafin tutar Nijeriya, amma fa ba ya kama da injiniyan gine-gine duk kuwa yana da ƙwarewarsa a fannin. Idan ka gan shi yana yin wasannin burgewa ne.

A ƙarshen mako ne wannan matashi mai shekaru 26 daga jihar Osun a kudu maso yammacin Nijeriya, ya fara wani abin bazata na rushe tarihin bajinta na “Yin Wasan tsafi na Mafi tsawon Lokaci na Mutum Guda”.

Wanda ke riƙe da kambin tarihin a yanzu, cewar Guinness World Records, shi ne Richard Smith daga Burtaniya, wanda ya yi wasan awa 30 da minti 45 ranar 7-8 ga Agustan 2004.

Fado na da niyyar haura tarihin ya kai awa 50. Sai dai ba don neman nuna bajinta da juriya ba ne, yana so ya sauya alaƙar Nijeriya da wannan wasa da ake yawan masa kuskuren fahimta.

Fado ya faɗa wa TRT Afrika cewa, “A duka sauran sassan duniya, sana’ar wasan tsafi daidai take da kowace sana’a. A Yammacin Duniya sana’a ce mai biliyoyin daloli.

Amma a Nijeriya wadda ɗaya ce cikin manyan cibiyoyin nishaɗantarwa a nahiyar Afirka, muna da masu wasan tsafi, ba guda ɗaya ba. Ni kaina na san kusan 50, amma yawan mutane ba su san da zamansu ba,” in ji Fado.

Shirin aiki

A shirye-shiryen goge tarihin baya na Richard, Fado ya kwashe sama da shekara guda yana ƙerawa da tattaro dabarun wasan, yana gina siddabarun wasan tsafi.

Ya ce, “Na shirya wasan tsafi salo 200 saboda duka ta ce ba za ka iya maimaita salo ba cikin awanni huɗu”.

Ya ƙara da cewa, “Mutane suna ganin abu ne mai sauƙi, amma sai da na kalli tarin darussan tsafi don zaɓar wadda zan shirya wa. Sayo kayan jere masu tsada, da gina su yake da wahala. Yawanci da kaina na gina su. Abu ne mai wahala yin aiki dare da rana”.

Shirye-shiryen ba su tsaya ga tsara rufa-ido ba kawai.

Ya cewa TRT Afrika, “Na fara atisaye kan shirin tun a Janairu— zuwa motsa jiki sau uku zuwa huɗu a mako. Na rage nauyi. Duk da zan iya siddabaruna ina zaune ko a tsaye matuƙar wasan bai tsaya ba.”

Ya ƙara da cewa, “Sai da na tabbata na samo kayan jerena masu kyau, saboda su ne abin da mutane za su fara gani idan sun zo. Ina so na far da burge ‘yan kallo tun da fari don su yaba da wasan tsafin.”

Yaƙar masu zargi

A wajen Fado, babban ƙalubalen shi ba shirya wasan ba, a’a, amma yaƙi da ƙyamar da ake wa wasan tsafi a Nijeriya.

“Mutane da dama har yanzu suna kallon wasan tsafi a matsayin irin tsafi mai cutarwa kamar juju, kamar yadda ake kiran sa a Nijeriya. Mutane sun fi son zahiri. Kenan idan mutum ya ga abu da ya kasa fayyacewa sai ya ce, wannan mugun tsafi ne”. In ji Fado

“Ana haka na koyo a wasan tsafi a YouTube. Kowa zai iya binciko ‘siddabarun wasan kati da masu koyo matakin farko’, ko ya sayo katin lale kuma ya fara da kansa. Kamar yadda ake koyon abin kiɗa ne instrument. Ana ɗaukar shekaru kafin a kai matakin da nake, amma bayanai na nan ga mai so.”

“Ina so wasan tsafi ya kai matakin da iyaye za su ce, ‘Kai, zo ka mana wasa don nishaɗantar da iyali.’ Wasan tsafi abin burgewa ne.”

Babbar Doka

Duk da buƙatar yin aiki tuƙuru, Fado ya ce mafi wahalar sharuɗɗan wasan daga hukumar Guinness World Records ba su shafi zama ba barci ba.

“Mafi tsaurin dokar ita ce samun ‘yan kallo a kowane lokaci — aƙalla mutane goma, ba tsare da tsaywa ba, ga shi kuma babu tabbacin samun su.”

Fado yana da digirin injiniyanci amma ya doge cewa dandalin wasan tsafi shi ma nasa ne a halin yanzu.

Amma fa Fado yana da tawaga mai tallafa masa waɗanda ke aiki don tabbatar da samun adadin ‘yan kallo da za su haura mafi ƙarancin sharaɗin.

“Mafi muhimmanci cikin tawagogin su ne na masu tsarawa, wato mataimaka wasan tsafi, da kuma masu alƙalancin wasan. Ba mu ɗauki kowane sharaɗi da wasa ba. Kowa ya karanta sharuɗɗan, gaba da baya don tabbatar da an bi su.”

Sai dai fado ya yi watsi da masu sukan waɗanda ke naman kafa tarihin bajinta na Guiness a baya-bayan nan.

“A Amurka da Indiya, a kullum mutane suna gwada kafa tarihin bajinta. Abu ne nomal. Idan ka ga za ka iya, ka ƙalubalanci kanka ta hanyar gwadawa saboda gwajin yana taimaka wa wajen isar da saƙonni masu kyau.”

Ajiye injiniyanci a gefe

Don da cewa yana da digiri a injiniyanci, Fado ya ce dandanlin wasan tsafi fagensa ne shi ma a dai halin yanzu.

“Duk wani ɗan kasuwa yana mayar da hankali kan abu ɗaya. In ƙaunar injiniyanci amma yanzu ina mai da hankali kan nishaɗantarwa. Ina da kamfanin gine-gine kuma ina gina shi a hankali. Da zarar sana’ata ta nishaɗantarwa ta yi ƙwari, zan faɗaɗa zuwa injiniyanci sosai.”

Yayin da ya gabatar da hujjojinsa ga hukumar Guinness World Records, Fado yana jiran da kuma yin kyakkyawan fata. Idan aka tantance shi, ya ce nasarar za ta haskaka wannan salon fasaha da ake yawan yi wa kallon raini, don mayar da shi mai tashe a Nijeriya.