Shekarar 2025 ta ƙare, amma ta ƙare ne tare da duk wata da'awar sassaucin ra'ayi ta ƙasashen duniya, da ƙawancen da ke tsakaninsu waɗanda suka ayyana su a matsayin tushen ɗabi'u, da kuma tsarin da ya dogara da dokoki, duka waɗannan aƙidu sun mutu a ƙarƙashin rusasshiyar Gaza.
A yanzu duniya na fuskantar wata tsohuwar ɗabi'a mai cike da rashin tausayi da aka sabunta: abin da ake kira Transactional Realism, wato cim ma biyan buƙata maimakon sadaukarwa.
Daga tsarin sabuwar dabarar Amurkahar zuwa neman tsaro a Brussels, wannan shi ne sabon tsarin siyasar duniya.
A wannan sabon matakin, ƙasashe —wadanda ke ikirarin cewa ba su da wani amfani na tunani mai kyau—suna kallon dabi'un jinƙai a matsayin abubuwan da ke cikin takardar lissafi da za a share.
A yanzu muradinsu ba na tabbatar da adalci ba ne, na ƙoƙarin magance matsaloli ne ta hanyar da za ta fi sauƙaƙa manufofinsu. A yanzu an daina gina ƙawance a kan manufofi na tushen ɗabi’u, sai dai a kan manufofi da haɗin gwiwar cuɗe-ni-in-cuɗe-ka.
A yayin da duniya ke komawa wata babbar kasuwar buƙata ta diflomasiyya, sannan ake maye gurbin jami’an diflomasiyya da dillalan manufofi, babban haɗarin da za a shiga a 2026 ba na ɓarkewar sabbin yaƙe-yaƙe ba ne, na danƙarar da matsalolin da ake ciki a Gaza da Ukraine ne a halin da suke ciki ta hanyar yin ciniki da cim ma yarjejeniyoyi na rashin imani da sadaukar da adalci.
Idan ƙsashen duniya ba su yi amfani da lamirin tausayi ba a shekarar 2026, to sakamakon hakan zai zama zallar ruɗani da a baya aka yi ta ɗage shi – wato za a shiga yanayi na rashin tausayi mai ɗorewa.
Katafaren teburin ciniki
Abin da ya ƙara sanya wannan tsari ya fi haɗari a shekarar 2026 shi ne rikice-rikice za su zamo ba matsalar ƙasa ɗaya ba kawai, abin da ya ci doma ba zai bar awai ba, kuma hakan zai mayar da tsarin ƙasa da ƙasa zuwa wani katafaren teburin ciniki.
Za a ga yanayin da ƙasashe za su janye daga batun Ukraine don mayar da hankali wajen cim ma wata manufa a Syria, za a iya maye shirun diflomasiyya kan batun Gaza da neman samun riba a fannin tsaron makamashi.
Wannan sabon tsarin diflomasiyyar yana nuna ɓaro-ɓaro irin jan layin da za a yi kan batutuwa, lamarin da zai mayar da duniya wata kasuwar buƙata ta son-rai inda za a dinga musayar komai ma da wani abin daban.
Ga alama yaƙin Ukraine shi ne zai fara zama abu na farko da za yi gwaji da shi a kan wannan sabon tsarin na duniya.
Yayin da fargaba ke ƙaruwa a manyan biranen Turai kuma kiraye-kirayen Amurka na "kawo ƙarshen wannan yaƙin" ke ƙaruwa, a 2026 za a iya fuskantar wani yanayi inda ra'ayoyin ƙa'idoji kamar mutunta yanki da cin gashin kai za su zama abin sadaukarwa ga gaskiyar yaƙin da ake yi a yanzu daga al'ummomin duniya.
Wannan sabuwar dabarar ciniki, wacce Amurka ke goyon baya, take kuma aiki a tunani irin na 'yan kasuwa, za ta mayar da hankali ne kawai kan rufe yarjejeniyar.
Yanayin ya ma fi yin tsananin a Gabas ta Tsakiya. A yayin da ake tsaka da kisan ƙre dangi a Gaza, duniya ta fi daukar batun Falasdinawa a matsayin batun aikin gina ta da samar da tsaro, maimakon na 'yancin siyasa da na ƙasa mai cin gashin kanta kawai.
Shirye-shiryen da za a ɗora a teburin a 2026 za su fifita tsaron Isra’ila da yiwuwar fitar da manyan masu ruwa da tsaki na duniya daga cikin rikicin ta hanya mafi sauƙi, maimakon fifita mutunci da ‘yancin Falasɗinawa.
Wannan tsarin wanda ke ɗaukar waɗanda aka yi wa kisan ƙare dangi a matsayin abubuwan da za a yi cinikin diflomasiyya a kansu maimakon a matsayin waɗanda aka yi wa kisan gilla ba, ba zai warkar da raunin ba; kawai za a rufe shi ne da siminti a cikin ruhin wannan sabon zamanin na ciniki.
Don haka a cikin wannan kasuwar buƙatar ta diflomasiyya a 2026, wa zai tsayawa marasa ƙarfi? Waye zai kare ‘yancin waɗanda tsarin ƙasa da ƙasa ya bari a baya?
Bisa sabo da ɗabi’ar da aka sani ta ƙarnin da ya wuce, mun mai da ido da hankulanmu kan hukumomin da ke kan tsarin sassaucin ra’ayi kamar su Majalisar Ɗinkin Duniya.
Sai dai, abubuwan da suka faru a 2025, musamman ma kisan ƙare dangi na Gaza, sun tabbatar da rashin ɗa’a da gazawar aiwatar da ayyuka na irin waɗannan hukumomi.
Ka'idojin ƙasashen duniya a yau suna aiki ne kawai a matsayin masu kula da yanayin da ake ciki.
Hukunce-hukuncen Kotun Duniya (ICJ) ba su wuce abubuwan karatu na jami'o'in shari'a ba akwai. Cibiyoyi da hanyoyin ƙarnin da ya gabata ba sa ma ɗauke da ƙananan bayanai a kan teburin shugabanni a duniyar gaskiya ta ciniki ba.
Saboda haka, neman lamiri na duniya a cikin waɗannan hanyoyi marasa tasiri aiki ne mara amfani. Cibiyoyi sun miƙa wuya ga aiwatar da wannan tsari. Adalci na duniya ba batun tsarin mulki ba ne, sai dai wani abu na son rai.
Ƙarfin shugabanni da fafutukar masu bore
Ana buƙatar sabbin masu ruwa da tsaki don su cike wannan giɓin. A 2026, akwai yiwuwar wasu manyan abubuwa uku su bijiro a matsayin muryoyin marasa ƙarfi.
Na farko zai kasance ƙasashen da da gangan suka sanya kansu a matsayin masu ɗa'a - ƙasashe waɗanda ke neman tasiri ba kawai ta hanyar ƙarfin tattalin arziki ko soja ba, har ma ta hanyar halalcin ɗa'a da kuma jajircewa ga dabi'un da suka shafi ɗan’adam.
Yawancin ƙasashe masu tasowa a Kudancin Duniya, daga Afirka ta Kudu zuwa Brazil da kuma daga Turkiyya zuwa Indonesia, suna ƙara tsara muhawarar duniya.
Ba wai kawai haɗin gwiwa ce mai sassauci wadda ke buƙatar ƙarin iko na tattalin arziki ba, amma suna da yuwuwar zama shugabanni wajen ayyana ƙa'idodi na duniya masu adalci da haɗaka.
Dole ne waɗannan ƙasashe su ɗauki nauyin zama masu bin diddigin ɗabi'a, suna bayyana giɓin adalci da ke tattare da tsarin.
An fallasa ikirarin Turai na ɗaukar matsayi na ɗabi'a a ƙarnin da ya wuce a matsayin munafunci, wanda hakan ya haifar da buƙatar wata ƙungiya don cike wannan gibin.
Misali, Afirka ta Kudu ba wai kawai ta nuna fafutukar neman 'yancin kai ba ne; ta hanyar amfani da dokokin Ƙasashen Yamma a Hague kan kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a Gaza, Ƙasashen Yamma sun yi shiru, kuma sun karya garkuwar da ba za a iya shiga ba ta rashin adalci.
Hakazalika, matsayar Shugaba Erdogan, ta kalubalantar shirun da duniya ta yi kan Gaza da kuma goyon bayan da ba ya misaltuwa ga manufar Falasdinu, ba wai kawai kalaman baki ba ne; adawa ce ta tsari inda "duniya ta fi biyar girma" ta hadu da diflomasiyyar jinƙai ta zahiri a kasa.
Yayin da ake sanya hannu kan yarjejeniyoyi masu amfani a shekarar 2026, waɗannan ƙasashe su ne kawai ƙarfin da za su iya ƙara bayanin jinƙai ga waɗannan rubuce-rubucen da kuma yin aiki a matsayin hanyar ƙarfafa gwiwa.
Na biyu shi ne jagoranci mai cike da jarumtaka. A cikin duniyar ciniki ta 2026, komai zai yi tsada, amma shugabanni masu jarumta za su ɗaukaka ƙima.
Shugabanci na gaske a wannan lokacin yana nufin tsayawa kan ƙa'idodi da iyakoki bayyanannu na ɗabi'a, ko da kuwa yin hakan ba shi da sauƙi, mai tsada, ko kuma mai illa ga dabaru.
Shugabannin da ke ganin 'yan gudun hijira a matsayin mutane ba wata haja da za a yi cinikinta, kuma waɗanda suka ayyana iyakoki ba wai kawai a matsayin ganuwar tsaro ba, har ma a matsayin layukan lamiri, su ne za su tantance makomar shekarar 2026.
Na uku, kuma wataƙila mafi mahimmanci, shi ne ‘yan gwagwarmaya daga masu bore zuwa ƙungiyoyin fararen-hula. Duk da cewa Ƙasashen Yammacin dDuniya sun fuskanci bankaɗa da bore daga ‘yan ƙasashensu, Istanbul ta fita zakka daga irin wannan lamari.
Taron magoya bayan Falasɗinu na ranar 1 ga Janairu a kan Gadar Galata ba wai kawai al'ada ce mai maimaita kanta ba. Bayyanar lamiri ce da aka gabatar wa tsarin duniya a farkon sabuwar shekara.
2026: Matsaloli
Yadda duniya ke mayar da martani ga wahalhalun da ake sha a Gaza zai fi muhimmanci a tarihi fiye da yadda jami'an diflomasiyya ke yin yarjejeniyoyi cikin sauri ko da wayo.
Duk da cewa a babin cinikiyya ana iya ɗaukar Falasdinawa a matsayin wani ɓangare na tsaro ko aikin gini, inda za a samar da kwanciyar hankali na ɗan lokaci, duk wata yarjejeniya da ba ta haɗa da adalci ba a zahiri ba to wani abu ne da ke ƙara ta'azzara rikici.
A wannan gaɓar, alhakin tarihi ya rataya a wuyan manyan ƙasashe masu ɗa’a da kuma waɗanda suka san me suke yi daga Kudancin Duniya da suka samar da wani shiri a inda tsarin ƙasa da ƙasa ya gaza.
Taswirar da za a bi a shekara mai zuwa dole ne ta zama tsararriya, ba wai burin ɗabi'a ba. Aikin waɗannan masu ruwa da tsaki ba wai kawai gabatar da tsarin gine-gine ba ne wanda ya haɗa da adalci a Gaza a matsayin zaɓi a teburin ba.
Dole ne a gina zaman lafiya mai ɗorewa, ba a matsayin fifiko ba kawai, har ma a matsayin mafita ɗaya tilo daga wannan rikicin.













