Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi Allah wadai da kisan kiyashi da aka yi a Al Fasher da ke Sudan, yana mai cewa ya zama dole a kare yankin ƙasar da martabarsa.
“Babu wanda ke da zuciya a kirjinsa—ba dutse ba—da zai iya aminta da kisan kiyashin da aka yi wa fararen hula a Al Fasher da ke Sudan, a 'yan kwanakin nan. Ba za mu iya yin shiru kan wannan ba,” in ji Erdogan a jawabin buɗe zaman taro na 41 na Kwamitin Harkokin Tattalin Arziki da Kasuwanci (COMCEC) na Kungiyar Hadin Kan Musulunci (OIC) a Istanbul a ranar Litinin.
Ya jaddada cewa ya zama dole a kare yankin Sudan, ikonsa da 'yancinsa, tare da nuna muhimmancin tsayawa tare da al’ummar Sudan, yana kira ga al’ummar Musulmi na duniya su ɗauki nauyi wajen kawo karshen zubar da jini.
“Yana da matukar muhimmanci mu ba mutanen Sudan goyon baya a cikin waɗannan lokutan da suke fuskantar jarrabawa, mu ci gaba da bayar da taimakon jin kai da tallafin ci gaba,” in ji Erdogan.
“Isra'ila tana da mummunan tarihi”
Da yake magana kan yakin Gaza, shugaban na Turkiyya ya nuna cewa kungiyar gwagwarmayar Falasɗinu, Hamas, tana da niyyar bin yarjejeniyar tsagaita wuta, yayin da Isra'ila ke da mummunan tarihi.
Isra'ila ta kashe fiye da mutane 200 marasa laifi tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, kuma ba ta dakatar da mamayewa da hare-hare a Gabas ta Yamma ba, in ji shi.
“Ba za mu yarda da yunkurin mamaye Gaɓar Yamma ba, sauya matsayin birnin Kudus, ko duk wani yunkuri na cutar da tsarkin Masallacin Al-Aqsa ba,” in ji Erdogan.

















