Rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) ta ce an kashe 'yan ta'adda fiye da 40 a hare-haren sama da aka kai a yankunan Azir da Musarram na jihar Borno, lamarin da ya dakile shirin kai hare-hare kan al'ummomin fararen-hula.
Da yake bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, Kakakin NAF, Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an kai hare-haren ne a ranakun 15 da 16 ga Janairu.
Ejodame ya bayyana cewa jiragen saman NAF da ke aiki a karkashin rundunar sojin sama ta Operation Hadin Kai ne suka kai hare-haren, bayan samun bayanan sirri masu inganci kan zirga-zirgar 'yan ta'adda da kuma barazanar da ke gabatowa ga al'ummomin da ke kusa.
A cewarsa, karin bincike ya nuna cewa 'yan ta'adda suna kokarin sake taruwa a karkashin bishiyar da ke kusa, wanda hakan ya haifar da samun nasara a hare-haren saman da aka ƙddamar a kansu da suka kashe da dama daga cikinsu.
Sanarwar ta ce, "Binciken da aka yi bayan kai hare-haren ya tabbatar da cewa babu wata barazana da za a iya fuskanta, yayin da bayanan da aka samu daga sojojin ƙasa da hukumomin yankin da kuma majiyoyin al'umma suka nuna cewa an samu raguwar kasancewar 'yan ta'adda da kuma dawo da kwanciyar hankali."
"A farkon ranar 15 ga Janairu, jiragen sama na NAF sun yi nasarar dakile hare-hare a Musarram a yankin Tumbuns bayan da bayanan sirri suka nuna cewa 'yan ta'adda sun taru a kan kwale-kwale don kai hare-hare a yankin Baga da Fish Dam.
"Da isowar jirgin, sai ya hango kwale-kwale kimanin 10 ɗauke da fiye da 'yan ta'adda 40 da ake zargi, wadanda ke tafiya su da yawa, lamarin da ya jefa su cikin rudani."
"An bi wasu daga cikin waɗanda suka tsere an kuma kashe su, yayin da wasu kuma da suka sake taruwa a wani yanki su ma aka ƙaddamar musu, wanda hakan ya sa aka wargaza wurin da 'yan ta'adda ke taruwa," in ji shi.
A nasa bangaren, Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya sake jaddada kudirin rundunar sojin saman na samar da tallafin sama mai inganci ga sojojin kasa a kan lokaci.
Aneke ya ce ayyukan sun nuna ingancin karfin sojin sama da leken asiri ke jagoranta da kuma hada kai tsakanin sama da kasa wajen hana 'yan ta'adda yin kataɓus.
Ya tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa za a ci gaba da matsin lamba kan 'yan ta'adda yayin da rundunar sojin ƙasar ke ci gaba da kokarin rage karfinsu da kuma daidaita al’amura a yankunan da abin ya shafa.











