Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya jinjina wa sojojin ƙasarsa bisa jarumtar da suka nuna cikin hanzari a ranar Lahadi wajen hana yin juyin mulki a ƙasar Benin mai maƙwaftaka.
Wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban ƙasar ya fitar ta ambato Shugaba Tinubu yana cewa "sojojin sun hanzarta wajen mayar da martani game da buƙatar da gwamnatin Benin ta miƙa ta ceto dimokuraɗiyyarta ta shekara 35."
Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya ɗauki matakin bayan gwamnatin Jamhuriyar ta buƙaci hakan sau biyu.

"Da farko Tinubu Shugaba Bola Tinubu ya umarci jiragen yaƙin Sojojin Saman Nijeriya su shiga ƙasar Benin inda suka ƙwace ikon sararin samaniyarta don taimakawa wajen daƙile masu iƙararin juyin mulkin da ke gidan talbijin na ƙasar da ma wani sansanin soji da suka sake taruwa," in ji sanarwar.
"A buƙata ta biyu kuma hukumomin Benin sun buƙaci yin amfani da kayan aikin rundunar sojin sama ta Nijeriya wajen tattara bayanai da kai agajin gaggawa bisa jagorancin hukumomin Benin."
Kazalika gwamnatin Benin ta buƙaci dakarun ƙasa na Nijeriya su “aiwatar da ayyuka bisa umarnin hukumomin Benin domin kare hukumomin da ke ƙarƙashin kundin tsarin mulki tare da daƙile ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai."
















