Mayakan Houthi na Yemen sun ba da alamar dakatar da kai hare-hare kan Isra’ila da kuma jiragen ruwa a Bahar Rum biyo bayan yarjejeniyar tsaigata wuta ta Gaza da aka cim ma, wadda ke tangal-tangal.
A wata wasiƙa da mayakan suka aika wa rundunar sojin Qassam ta Hamas wadda aka yada a daren ranar Litinin, sun bayyana dakatar da kai hare-hare da suke kaiwa cak.
"Muna sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa kana muna bayyana cewa idan abokan gaba suka ci gaba da kai hari Gaza, za mu dawo da ayyukan sojinmu kan Yahudawa, kuma za mu dawo da haramcin zirga-zirgar jiragen ruwa na Isra'ila a Tekun Bahar Rum da kuma na Larabawa," in ji wasikar.
‘Yan Houthi dai sun yi suna a duniya a lokacin yakin kisan kare dangi da Isra'ila ke yi Gaza inda a bangare guda su kuma suke kai hare-hare kan jiragen ruwa da Isra'ila, wanda suka ce suna yi ne don tilasta wa Isra'ila ta dakatar da yakinta.
Tun da aka cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta wadda ta soma aiki daga ranar 10 ga Oktoba, ƙungiyar ba ta sake ɗaukar alhakin kai wani hari ba.
Kawo yanzu dai mayakan Houthi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan cewa sun dakatar da kai hare-harensu yankin.





















