Daga Firmain Eric Mbadinga
Abin da ke shiga a cikin bolarku zai iya yiwuwa shi ne abin da Benjamin Ndoubanadji ke nema.
Ndoubanadji, wanda injiniya ne, ya yi iya bakin ƙoƙarinsa domin sauya tsarin yadda jama’ar ƙasarsa ta Chadi ke zubar da shararsu, wato sabunta bolar da miliyoyin jama’a ke zubarwa zuwa wani abu mai amfani.
A matsayinsa na ɗan kasuwa wanda ya mayar da hankali kan ƙirƙire-ƙirƙire, ba wai kawai yana taimakawa wurin kwashe bolar da ke neman addabar unguwanni ne da ke a N’Djamena babban birnin Chadi ba kawai.
Kamfanin GAZINT na su Benjamin, na tattarawa da sarrafa bola zuwa biogas, wanda a halin yanzu shi ne makamashin da dubban mutane suka dogara da shi a N’Djamena.
Biogas makamashi ne wanda ake samarwa daga bola da matattun tsirrai da takin gona da lalatattun kayayyakin abinci.
Wani ƙarin tagomashi na amfani da wannan sinadarin shi ne ba ya gurɓata muhalli, inda amfani da shi yake rage fitar da hayaƙi mai gurɓata muhalli ta hanyar daƙile sinadarin methane mai guba kafin ya lalata muhalli.
Hangen nesa
Gudunmawar da GAZINT ke bayarwa game da yanayin makamashin cikin gida ya yi daidai da wani shiri na hukumar raya ƙasa ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) na ƙarfafa yawancin ƙasashen Afirka irin su Burundi da Mauritaniya su saka hannun jari a wannan fanni da rage amfani da makamashi mai gurɓata muhalli.
"Burina shi ne na haɗa hanyoyin samar da makamashi mai ɗorewa don taimakawa wurin sauyin makamashi da rage fitar da sinadarin carbon. Na ƙuduri aniyar yin tasiri ga al'umma da muhalli yadda ya kamata,” kamar yadda Benjamin ya shaida wa TRT Afrika.
Yayin da yaje haɗa na’urar girki ta biodigester, a bayyane take cewa Benjamin jigon falsafar Benjamin shi ne yin komai a sauƙaƙe. Wurin sarrafar ta ƙunshi injin ƙarfe tare da wani wuri inda ake dagargaza shara da kuma wata ƙofa da ake fitar da biogas ɗin.
Wurin sarrafa gas ɗin nasa na iya samar da kilogram 6 zuwa 12 daga shara bola mai nauyin kilo 200.
Rashin daidaito a makamashi
Bankin Duniya ya bayyana yadda ake samun rashin daidaito ta ɓangaren samar da makamashi a duniya baki ɗaya.
A shekarar 2022, mutum miliyan 685 ne ba su da wutar lantarki, inda kuma mutum biliyan 2.1 ne suka dogara wurin girki da makamashi mai guba.
Duk da cewa biogas ɗin GAZINT ana amfani da shi ne wurin girki, Benjamin na son ƙara yawan gas ɗin da ake samarwa domin ya zama wata hanya ta biyu ta samun wutar lantarki ga Chadi,
“Na yi sa’ar aiki a wurare biyu waɗanda suka haɗu (ɓangaren injiniya na kanikanci da kuma makamashi) wanda suke burge ni,” kamar yadda ya bayyana.
Kafin ya ƙaddamar da kamfaninsa, Benjamin ya shafe shekaru yana sa ido kan yadda ake tafiyar da bola da ake zubarwa domin samun muhimman bayanan da za su taimaka wa bincikensa.
Ya gano cewa akasarin lokaci, bolar da ake zubarwa ana kwashe su zuwa wuraren da ake tara bola inda take lalacewa maimakon a sabunta.
Ganin cewa mazauna N’Djamena kaɗai suna samar da tan 600 na bola a kullum, Benjamin da kuma abokan aikinsa na samun kayayyakin aikinsu daga ciki. Duk da haka samun irin wannan sharar ƙalubale ne, wanda GAZINT ke son sauƙaƙawa ta hanyar amfani da jama’ar gari domin taimaka musu.
Kamfanin Benjamin ya sayar da na’urorin girki na biogas 200 a cikin wata ɗaya a bana.
Haka kuma kamfanin na shirin raba sauran kayayyakin da yake sayarwa ciki har da abin girki na gawayi maras gurɓata muhalli.
“Ina kallon kaina a matsayin mai kare muhalli,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
















