Turkiyya ta yi kira da a gaggauta dakatar da rikici a birnin Al Fasher da yankunan da ke kewaye da shi a Sudan.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta kuma bukaci a samar da amintattun hanyoyin wucewa, da ba da damar isar da tallafin jinƙai ba tare da wani cikas ba, da kuma kawo ƙarshen hare-hare kan fararen hula da ba su ji ba su gani ba.
Sanarwar ta bayyana cewa Ankara na bin abubuwan da ke faruwa a Sudan da matukar damuwa, kuma tana goyon bayan sanarwar da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa ta fitar kan lamarin. Ma’aikatar ta yi Allah wadai da munanan laifukan da ake aikata wa kan fararen hula a Al Fasher, wanda ya fada karkashin ikon dakarun RSF (Rapid Support Forces) a ƙarshen mako.
Ma’aikatar ta sake jaddada cikakken goyon bayan Turkiyya ga haɗin kan Sudan, ‘yancin ganshin kanta, tare da jaddada muhimmancin tattaunawa don samun mafita mai ɗorewa kan rikicin.
Tun daga watan Afrilun 2023, an ci gaba da yaƙin basasa tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF. Dubban mutane sun rasa rayukansu, yayin da fiye da mutum miliyan 14 suka rasa matsugunansu sakamakon rikicin.
















