Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya na kallon Syria mai dunkulallen yanki a matsayin muhimmiyar kasa ga kwanciyar hankali da wadata a yankin, yana mai jaddada jajircewar Ankara ga 'yancin kai da hadin kan al'ummar Syria.
"Syria ta ‘yan Syria ce," in ji Erdogan a ranar Litinin a wani jawabi da aka watsa ta talabijin bayan taron majalisar ministoci na mako-mako, yana mai jaddada cewa kasar gida ce ga al'umma daban-daban wadanda dole ne a kare hakkoki da hadin kai.
Shugaban kasar Turkiyya ya ce ya shaida wa takwaransa na Syria cewa Turkiyya za ta ci gaba da goyon bayan kasar a yaki da ta'addanci, yana mai cewa, "Ba za mu yi watsi da al'ummar Syria ba."
Erdogan ya yi maraba da sabuwar yarjejeniyar da aka cim ma tsakanin gwamnatin Syria da kungiyar ta'adda ta YPG, yana mai cewa:
"'Yan Syria sun bayyana suna farin ciki da yarjejeniyar jiya, sai dai wasu 'yan tsirarun wakilai da ke neman kafa kasa a cikin wata kasa".
"Zamanin ta'addanci a yankin ya kare," yana mai jaddada cewa, "dangane da tsagaita wuta, dole ne a cika cikakkun yarjejeniyoyin hadewa tare da kauce wa kura-kurai".
Ya kuma yaba wa sojojin Syria saboda yadda suka yi taka tsantsan wajen kai farmakai kan 'yan ta'addar YPG don kwace yankunan arewa maso-gabashin ƙasar duk da tsokanar da ake yi musu.
"Yadda sojojin Syria suka gudanar da wannan aiki mai muhimmanci abin yabawa ne. Duk da tsokana, sojojin Syria sun ci nasara jarrabawa, suna guje wa ayyukan da za su sa su yi kuskure lokacin da suke kan gaskiya," in ji shi.
Ya jaddada cewa Syria ta dukkan mutanen kasar ce.
"Syria ta mutanen Syria ce a dukkan bangarori daban-daban, ciki har da Larabawa, Turkmen, Kurdawa, Alawiyawa, Sunni, da Druzes."
Shugaban Turkiyya ya sake nanata cewa Turkiyya, a matsayin "‘yar uwa, maƙwabciya, kuma abokiya" ga mutanen Syria, ta ci gaba da kasance wa tare da su a lokutan rikici da wahalhalu.
Ya ƙara da cewa Ankara za ta yi adawa da duk wani mataki da nufin lalata haɗin kan Syria ko mutuncin yankinta.
"Ba za mu yarda da duk wani yunƙuri na ɓata wannan ba," in ji Erdogan, yana mai nuna ƙudurin Turkiyya na hana shirye-shiryen da za su iya wargaza Syria ko kuma hargitsa yankin.
Erdogan ya bayyana tashin hankalin da ke faruwa a Iran a matsayin "sabuwar jarrabawa" ga Tehran, yana mai alƙawarin cewa Turkiyya za ta "kalubalanci duk wani shiri" da zai jefa yankin cikin rudani.
"Mun yi imanin cewa, tare da manufofin da suka fi ba da fifiko ga tattaunawa da diflomasiyya, 'yan'uwanmu na Iran, da yardar Allah, za su shawo kan wannan lokaci mai cike da tarkuna."





















