Yayin da awanni ne suka rage a ayyana wanda ya zama gwarzon ƙwallo ƙafa na duniya a bana, kocin tawagar ƙasar Masar, Hossam Hassan ya yi kira da a girmama tauraron ƙwallo na ƙasar, Mohamed Salah.
Salah na cikin jerin taurarin ‘yan ƙwallon da za a zaɓa don fitar da wanda zai lashe kyautar Ballon d'Or ta shekarar 2025.
Da yake ayyana Salah a matsayin ‘gwarzo abin koyi, Hassan ya ce ɗan wasan da ke buga wa Liverpool ta Ingila, abin koyi ne ga masu neman nasara a fannin ƙwallo a duniya.
A kakar bara, Mohamed Salah dai ya ciyo wa Liverpool ƙwallaye 34 a duka gasanni kuma ya taka rawar gani wajen taimaka wa ƙungiyarsa lashe kofin Firimiya.
Da wuya Salah ya kai labari
A maraicen yau Litinin ne za a gudanar da bikin ba da kyautar gwarazan ƙwallon ƙafa maza da mata a wani ƙasaitaccen biki da za a yi a birnin Paris na Faransa.
Sai dai duka da ƙwazon da ya nuna a bara, masana ƙwallo na ganin zai yi wuya Salah mai shekaru 33 ya kai labari.
Hasali ma, ɗan wasan Paris Saint-Germain ta Faransa, Ousmane Dembele ne ake kyautata zaton zai ɗauki kambin a bana.
Baya ga Dembele, akwai matashin ɗan wasan Barcelona ɗan asalin Saifaniya, Lamine Yamal da kuma wani ɗan wasan Barca ɗan asalin Brazil, Raphinha da ke gaba da Salah a cancantar lashe kyautar.