Turkiyya a ranar Lahadi ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Afghanistan da Pakistan, wadda aka cim ma a yayin tattaunawar da aka gudanar a babban birnin Qatar, Doha, wadda Turkiyya da Qatar suka shiga tsakani.
A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta kuma yaba wa matakin da Islamabad da Kabul suka ɗauka na kafa hanyoyin da za su inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin ƙasashen biyu.
“Turkiyya za ta ci gaba da goyon bayan ƙoƙarin samar da zaman lafiya mai ɗorewa da kwanciyar hankali tsakanin waɗannan ƙasashe biyu da kuma yankin baki ɗaya,” in ji ma’aikatar.
Ma’aikatar ta kuma jinjina wa Qatar saboda rawar da ta taka wajen karɓar baƙuncin da kuma sauƙaƙa tattaunawar.
A baya a ranar Lahadi, Pakistan da Afghanistan sun tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta nan take.
Tashin hankali a kan iyaka ya ƙaru bayan Pakistan ta kai hare-hare ta sama a lardin Paktika na Afghanistan a daren Juma’a, wanda Kabul ta ce ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama, yayin da jami’an ɓangarorin biyu ke Doha don tattaunawa.