| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ƙwace miyagun ƙwayoyi da aka yi safararsu daga Nijeriya
Hukumomin na Nijar sun kama wani mutuƙin babur ɗauke da kilo 30 na tabar wiwi da wasu miyagun ƙwayoyi 15,000 a wani shingen bincike da ke Dosso.
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ƙwace miyagun ƙwayoyi da aka yi safararsu daga Nijeriya
An gano kilogram 30 na tabar wiwi da kuma ƙwayoyi guda 15,000 bayan binciken da aka yi / Actu Niger
8 Disamba 2025

Hukumomi a yankin Dosso na Jamhuriyar Nijar sun bayyana cewa an yi babban kamu na miyagun ƙwayoyi bayan jami’an jandarma a wani shingen bincike sun tsayar da wani mai babur da ke dakon miyagun ƙwayoyi masu yawa daga Nijeriya.

An kama mutumin ne a ranar Jumma’a, kuma an tabbatar da hakan a hukumance washegari da safe inda Magajin Garin Dosso, Squadron Leader Boubacar Ali China Goga ne ya tabbatar.

A cewar shugaban Rundunar Haɗin Gwiwa mai lamba 2, aikin ya fara ne kawai a matsayin binciken da suka saba na yau da kullum.

“Ranar Jumma’a, 5 ga Disamba, da ƙarfe 12:30 na rana, jami’anmu sun tare wani mutum da yake tafiya a kan babur na Kasea daga Nijeriya zuwa Kiota,” in ji shi.

An gano kilogram 30 na tabar wiwi da kuma ƙwayoyi guda 15,000 bayan binciken da aka yi a kayansa, waɗanda darajarsu ta kai kusan miliyan 3.5 na Kuɗin CFA.

Mataimakin Lauyan Gwamnati, Oumarou Ibrahim, ya yaba da “kyakkyawan aikin” jami’an jandarma, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin “gwargwadon abin da doka ta tanada.”

Magajin gari na Dosso, Ali China Goga, shi ma ya jinjina wa jami’an tsaro, inda ya bayyana mai safarar ƙwayoyin a matsayin “ɗanta’adda ɗauke da makaman hallaka al’umma sannu,” kalma mai ƙarfi da ta nuna illar safarar miyagun ƙwayoyi a yankin.

Duk da cewa wannan samame nasara ce ga jami’an tsaro na yankin, ya kuma sake nuna yadda matsalar safarar ƙwayoyi daga Nijeriya zuwa tsakiyar Nijar ta zama wani babban ƙalubale - hanyar da aka ce har yanzu tana da matuƙar wuya a katse ta.