Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta rufe kamfanonin samar da tsaro masu zaman kansu 400 a lokaci ɗaya ta hanyar wata doka da ministan tsaron cikin gida Manjo Janar Mohamed Toumba ya rattaba wa hannu.
Bayanai daga hukumomin Nijar sun ce an ɗauki wannan mataki ne a ƙoƙarin gwamnatin na kawo ƙarshen shekaru da aka shafe na rashin tsari a fannin tsaro da ke da matuƙar muhimmanci.
Duk da cewa sanarwar ministan ba ta ba da hujja kan rufe kamfanonin ba, kafar watsa labarai ta Actu Niger ta ce an ɗauki matakin domin tsaftace tsarin samar da tsaron ƙasar.
Tun ranar 10 ga watan Yunin shekarar 2024 ne ma’aikatar tsaron cikin guda ta janye lasisi aikin kamfanoni uku na samar da tsaro: Securicom da GADNET Sécurité da kuma Manga Sécurité bayan sun nuna gazawa wajen gudanar da ayyukansu.
A hanlin yanzu waɗannan kamfanonin na cikin kamfanoni 400 da aka rufe har abada.
Yayin da wasu ke ganin wannan matakin a matsayin abin da zai janyo damuwa game da rashin ayyukan yi ga masu gadi, wasu na ganin matakin a matsayin abin da ake buƙata domin magance wani yanayi na rashin tabbas.
Ma’aikata da dama sun soki tsarin albashi da bai kai ya kawo ba da waɗannan kamfanoni ke bayarwa, wanda galibi bai kai 50,000 CFA ba a ko wane wata, da kuma shafe sa’o’i masu yawa a aiki da rashin kariya kan matsalolin rayuwar yau da kullum.
Dokar watan Fabrairun shekarar 2025
Domin cike giɓin doka da ke a fannin, ranar 7 ga watan Fabrairun shekarar 2025 ne majalisar ministocin ƙasa ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar Janar Abdourahamane Tiani, ta amince da dokar tsara ayyukan kamfanonin tsaro masu zaman kansu.
Kawo yanzu, waɗannan kamfanonin suna aiki ne kan izini na wucin-gadi ba tare da tsare-tsare na sa ido ba. Wannan ne ya sa wasu mutane masu barazana ga tsaron jami’ai suka shiga harkar, in ji rahotanni daga ƙasar.
Dokar ta samar da wani tsari mai ƙarfi ga kamfanoni na tsaro masu zaman kansu, inda ya ba da izinin na shekara biyar da ba za a iya musayarsa ba da wajabta bincike kan ɗabi’un shugabannin kamfanonin da sa ido sosai wajen riƙe makamai da kuma haramta musu yin ayyukan da doka ta ware wa dakarun ƙasar na FDS tare da kafa wata hukuma mai sa ido kan fannin gaba ɗaya.
Baya ga haka dokar ta bai wa dukkan kamfanonin da ke aiki lokacin wa’adin wata shida su cika sharruɗan ko kuma a rufe su.
Sabon zamani ga tsaron masu zaman kansu
Wannan tsarin dokar na ranar 18 ga watan Satumbar shekarar 2025 ya ƙunshi jerin kamfanonin da a aka ƙwace rajistarsu daga sanannu irin su Le Bouclier da Tigre Security Group da Lynx Security zuwa waɗanda ba sani ba. Saƙon dokar shi ne: gwamnati na karɓe iko kan wannan muhimmin fannin da bai kamata a bari da matsalolinsa ba
"Duk wanda ya saɓa wa tanade-tanaden wannan dokar za a yake masa hukunci da wannan dokar ta tanada ," in ji dokar.
Wannan matakin zai yi tasiri na tattalin arziƙi da na zamantakewa nan-take. Dubban masu gadi sun fuskantar rashin aikin yi yayin da ya zama dole wa kamfanonin da dama su nemi sabbin masu kamfanonin tsaro da za su ɗauka domin tabbatar da tsaronsu.