| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Nijeriya ba ta da kayan more rayuwa da ake buƙata don karɓar baƙuncin Gasar Kofin Duniya – Infantino
Shugaban hukumar FIFA ya bayyana cewa muhimmin abin da ake buƙata domin karɓar bakuncin gasar shi ne ingantattun kayayyakin more rayuwa, ciki har da filayen wasa, da filayen jiragen sama da ingantaccen tsarin sufuri.
Nijeriya ba ta da kayan more rayuwa da ake buƙata don karɓar baƙuncin Gasar Kofin Duniya – Infantino
Shugaban na FIFA ya bayyana cewa muhimmin abin da ake buƙata domin karɓar bakuncin gasar su ne ingantattun kayayyakin more rayuwa / AFP (Wire)
 

Nijeriya ba ta da kayayyakin more rayuwa da ake buƙata domin karɓar baƙuncin gasar cin kofin duniya ta FIFA a halin yanzu, musamman ta fuskar filayen wasanni, da filayen jiragen sama da hanyoyin sufuri, a cewar shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA), Gianni Infantino.

Infantino ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talbijin na Arise News, lokacin da aka tambaye shi ko Nijeriya na da ƙarfin karɓar baƙuncin babbar gasa kamar ta Kofin Duniya.

" A yanzu dai, ba ta da wannan damar. Amma nan gaba fa, me zai hana?" in ji shi.

Shugaban na FIFA ya bayyana cewa muhimmin abin da ake buƙata domin karɓar baƙuncin gasar su ne ingantattun kayayyakin more rayuwa, ciki har da filayen wasa, da filayen jiragen sama da ingantaccen tsarin sufuri.

Ya ce dole ne ƙasashen da ke son karɓar baƙuncin gasar su samar da waɗannan muhimman abubuwa bisa ƙa'idojin da suka dace.

Kazalika Infantino ya yi wa ƙasar kyakkyawan fatan na cewa za ta iya ƙarbar bakuncin gasar a nan gaba, yana mai cewa ƙasar na da albarkatu, da sha'awar ƙwallon ƙafa da kuma ƙudurin aiwatar da ayyukan raya filayen wasanni da su kai ka’idar FIFA.

Masu AlakaTRT Afrika - FIFA ta naɗa wa Nijeriya kwamitin mutum 5 don daidaita lamuran NFF, ciki har da Amokachi

Ya ce yana ganin ‘‘Nijeriya na da dukkan abubuwan da ake buƙata, ciki har da kuɗaɗe da ƙwazo, domin aiwatar da shirye-shiryen inganta filayen wasanni.’’

Haka kuma, ya yaba da wasu cibiyoyin wasanni da ya ziyarta a Nijeriya, musamman a Abuja da Warri, inda ya bayyana wani filin wasa da ya gani a matsayin mai kyau da ban sha'awa.

‘‘Misali, na ziyarci wata cibiyar horaswa a Abuja da Warri, sun yi kyau sosai’’ in ji shi.

Jawabin Infantino ya zo ne kwanaki kaɗan bayan ya kai ziyara domin duba aikin gina cibiyar fasahar ƙwallon ƙafa ta FIFA Forward a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, da kuma filin wasa na Warri City da aka gyara a jihar Delta.

Shirin FIFA Forward na bayar da tallafin kuɗi da na fasaha domin bunƙasa ƙwallon ƙafa a ƙasashe mambobin hukumar FIFA.

Nijeriya ba ta taɓa karɓar bakuncin gasar cin kofin duniya ba, duk da cewa ta halarci gasar a lokuta da dama, inda babban nasarar da ta yi shi ne kai wa zagayen 'yan 16 a wasannin shekarun 1994, da 1998 da kuma 2014.