Dakarun rundunar tsaron hadin gwiwa ta Operation HADIN KAI (OPHK) sun gano wani kabarin bai-ɗaya da ke dauke da gawarwakin 'yan ta'adda kimanin 20 da sojoji suka kashe a lokacin aikinsu a Timbuktu Triangle da ke Jihar Borno.
Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa daka fitar a ranar Laraba, daga Laftanar-Kanar Sani Uba, Jami'in Yaɗa Labarai na OPHK.
A cewar Uba, gano kabarin bai-ɗayan ya nuna ƙaruwar yawan asarar da 'yan ta'addan ke fuskanta sakamakon ayyukan soji.
"A wani ƙarin bayani game da asarar da 'yan ta'addan suka yi, sojoji sun gano kaburbura da ke ɗauke da kimanin gawarwakin 'yan ta'adda 20 da aka kashe a lokacin fafatawa da sojoji a Timbuktu Triangle kuma 'yan’uwansu ‘yan ta'addan suka binne su."
"Ganowar ya fallasa girman asarar da 'yan ta'adda suka yi kuma ya ƙara ɓata labaran farfagandar 'yan ta'adda," in ji Uba.
Sanarwar, wacce ta nuna wasu nasarorin da aka samu a ayyukan da ake gudanarwa, ta ce sojoji sun share kuma sun mamaye muhimman wurare na 'yan ta'adda a fadin dandalin Timbuktu, ciki har da Tergejeri, Chiralia, da kuma yankunan Ajigin/Abirma gaba daya.
A cewar sanarwar, a yayin aikin, sojoji sun yi mu'amala lokaci-lokaci da 'yan ta'adda da suka gudu, inda suka yi musu ruwan wuta mai yawa, wanda hakan ya yi sanadiyyar kashe 'yan ta'adda da dama.



















