9 Maris 2026
Kungiyar Izala mai hedikwata a garin Jos ce ta dakatar da Sheikh Alƙali Abubakar Salihu Zaria a farkon makon nan, bayan tuhumarsa da yin kalaman da ta ce sun “saɓa wa dokokinta” na wa’azi, bayan ya kwashe kimanin kwana 11 yana gabatar da tafsirin azumin Ramadan na bana.
